TUNAWA DA MARIGAYI ABUBAKAR RIMI.

A yau Lahadi 4 ga watan Afrilun 2021 ne tsohon gwamnan farar hula na farko a tsohuwar jihar Kano wato Marigayi Alh. Dakta Muhammad Abubakar Rimi CON, Yake cika shekara 11 da rasuwa.

Tarihin Rayuwar Sa A Takaice.

Marigayi Alhaji Abubakar Rimi shi ne Gwamnan Farar Hula Na farko a Jihar Kano an haife shi a shekarar 1940 a kauyen Rimi dake yankin Karamar Hukumar Sumaila a Jihar Kano.

Ya zamo gwamnan Jihar Kano a shekarar 1979 lokacin da aka mayar da mulki hannun farar hula a Jamhuriya ta biyu.

Yana cikin jigogin da suka kafa Jam’iyyar PDP
Alhaji Abubakar Rimi ya yi shura cikin fitattun ƴan Siyasa a Najeriya, Yayi karatun sa na Kos a Zaria, kuma ya samu takardar shedar zuwa jami’ar London, kasar England a 1972, Ya hada diflomar sa a kasar kuma ya samu shedar babban digri.

Rimi yana daga cikin mutanen da suka kirkiri jam’iyyar PRP a shekarar 1978 kuma an zabe shi a matsayin mataimakin jam’iyyar na kasa a taron ta na farko a jihar Lagos.

Abubakar Rimi an zabe shi a matsayin gwamnan tsohuwar jihar Kano a Oktobar 1979 har zuwa Mayun 1983.

A farko 1983 Rimi ya fita daga jam’iyyar PRP ya koma Nigerian People’s Party (NPP), A lokacin mulki Rimi ya yiwa jama’ar jihar Kano da Jigawa aikin da wani gwamna bai taba yi ba.

Muhammad Abubakar Rimi shi ya gina gidan jaridar jihar Kano Triumph, ya gina gidan Television na CTV Kano wanda ya koma ARTV yanzu, ya gina Kasco da kuma Knarda.

A 1993 Rimi ya zama ministan yada labarai sannan ya zama shugaban NACB da NSPMC.
Rimi ya fita daga Jam’iyyar PDP a 2006 ya koma jam’iyyar Action Congress (AC) amma a 2007 Rimi ya sake komawa PDP.

A watan Janairun 2006 wasu ƴan ta’adda suka shiga gidansa suka kashe masa matar sa Sa’adatu Abubakar Rimi.

RASUWAR MARIGAYI ALHAJI ABUBAKAR RIMI

Tsohon gwamnan Jihar Kano, Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi, ya rasu cikin daren Lahadi Ranar 4 ga watan 4 na shekarar 2010, A bayan da ƴan fashi suka tare su suka yi musu fashi dab da kauyen Darki, kusa da garin Takai a kan hanyarsu ta komawa Kano daga Jihar Bauchi Bayan halartar Bikin Nadin Sarauta a Garin Das.

Marigayi Abubakar Rimi, bai ji rauni lokacin fashin ba, amma ya isa gida yana fama da ciwon ƙirji. An ce daga nan aka garzaya da shi zuwa asibitin Mallam Aminu Kano, inda ya cika a cikin daren.

Kuma aka yi jana’izar sa da hantsin ranar Litini 5 ga wata 4 a shekarar 2010 a Kano, A karshe muna addu’ar Allah Ubangiji ya jikansa, Allah ya kai rahama kabarin sa, ya masa sakayya da gidan aljanna firdausi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here