Advert
Home Sashen Hausa TUN SHEKARAR ALIF NA 968 BABU NAJERYA ACIKIN JERIN ƘASASHE: Sheikh Yaqub...

TUN SHEKARAR ALIF NA 968 BABU NAJERYA ACIKIN JERIN ƘASASHE: Sheikh Yaqub Yahaya katsina

TUN SHEKARAR ALIF NA 968 BABU NAJERYA ACIKIN JERIN ƘASASHE: Sheikh Yaqub Yahaya katsina

A wajen taron Mauludin Annabi S.A.W da ɗiliban makaranta suka shirya a katsina

Daga Isma’il Abubakar Idris Katsina.

Tin Alif na 968 babu Kasar Najeriya cikin jerin tsarin Kasashe kamar yadda sauran kasashen duniya suke; Dalili shine kowace Kasa dole sai ta ginu bisa wasu ginshikai guda (4) shine zata zama Kasa.

1)Unity, Hadin kan Kasa.

2)Peace, Zaman Lafiya.

3)Faith, Imani da kasa.

4)Progressive. Cigaban Kasa.

1 Tundaga kashe Amadu Bello Unity hadin kai ya tashi a Najeriya domin dan kudu an ginashi bisa wani kabilanci na daban tsakaninshi da dan arewa sai kiyayya da juna, hakan yasa ake rigimar Kudu da Arewa kamar yadda muke gani a yanzu.

Shikuma dan arewa an gina shi ne bisa tarbiyyar addini. Domin hadin kan dan kudu da dan Arewa yasa aka Kir-kiri NYSC idan dan arewa ya gama karatu yaje kudu bautar Kasa, idan dan kudu ya gama karatu yazo arewa bautar kasa.

Malam minu kano yana cewa “Najeriya 1 Amma kowa yasan gidan ubansa”.

2) Peace, zaman lafiya : abin da mutanen baya suka kasa samarwa tun lokacin baya, yanzu shine mutane irinsu Buhari zasu iya samarwa, yanzu babu zaman Lafiya a kowane yanki, ka tambayi Mutanen Maiduguri, ko mutanen Birnin gwari da mutanen yankin Kaduna ko Mutanen Batsari yankin Katsina ta ina aka samu zaman lafiyar? Duk da yawan Soja, Dan sanda, Civil defence da sauransu amma ina zaman lafiyar yake?

3) Imani sadaukar da rayuwa dan kare kasa, yanzu wazai yarda ya bada ransa sabida Najeriya bayan masu mulki sun sace kudin al’umma sunkai gidajensu da kasashen wajen, duk mai mulkin da yaci zabe saiya mai da Riba a mulkinsa, kasa ta lalace, ina yarda ko imani da Kasa yake anan?

4) Prograssive, Cigaba : ina cigaban da muke samu a Najeriya bayan cigaban mai gina rijiya,  Saudiyya da Najeriya tare aka samar masu jirgin sama amma yanzu Saudiyya nada jirgin sama fiye da 1000, Najeriya ko fiffike batada shi. Mudauki misali da nan garin Katsina da akwai gidan kafet inda akeyin kafet da gidan man gyada da gidan rodi, yanzu ina suke..?, kaje ka bincika kowace Jaha ka gani duk zaka samu ire-iren wannan ina cigaban yake?

Damuwar mu ba Najeriya bace ko kudu da arewa a’a damuwar mu addini, duk duniya masu ilmin kasa ke cetan kasarsu amma Najeriya masu ilminta ke kasheta, Yanzu a Najeriya duk mai Certificate ya samu tikitin yin sata yadda yakeso.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

An Naɗa Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan A Matsayin Shugaban Jami’ar Cavendish Ta Kasar Uganda (CUU)

An Naɗa Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan A Matsayin Shugaban Jami’ar Cavendish Ta Kasar Uganda (CUU) Mukamin na ‘Chancellor’ na jami’ar ta CUU ta...

“Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Zai Gana da Dukkan Shuwagabannin Kananan Hukumomi a Kasar Nan”

LABARI DA DUMI-DUMIN SA! "Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Zai Gana da Dukkan Shuwagabannin Kananan Hukumomi a Kasar Nan" Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai sanya labule da...

Shugaba Buhari Ya Baiwa Kwamitin Rage Talauci Umurnin Gaggauta Ceto Mutane Milyan Dari Daga Talauci A Najeriya

Shugaba Buhari Ya Baiwa Kwamitin Rage Talauci Umurnin Gaggauta Ceto Mutane Milyan Dari Daga Talauci A Najeriya A ranar Talata, 22 ga watan Yuni, 2021,...

Iran Carries Out 1st Remote Surgery with Home-Made Robot

Iran Carries Out 1st Remote Surgery with Home-Made Robot I am sharing this with Friends because the Western MainStream Media (MSM) will NEVER show you...
%d bloggers like this: