Tuƙin Ganganci: Ankai ɗan Marigayi Yar’adua kurkuku

Aminu Yar’Adua: An kai ɗan marigayi Shehu Yar’Adua kurkuku

Wata kotun majistiret da ke Yola babban birnin jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya ta kai Aminu Yar’Adua, dan marigayi Shehu Musa Yar’Adua, gidan yari.

Kamfanin dillancin labarai na NAN ya rawaito cewa kotun ta aika da matashin, mai shekara 36, gidan maza ne bisa zarginsa da kisan mutum hudu yayin wani hatsarin mota da ya auku a birnin Yola.

Aminu Yar’Adua, dalibi ne a Jami’ar American University of Nigeria (AUN) Yola, kuma kotun tana zarginsa ne da yin tukin ganganci ranar 23 ga watan Yunin 2021.

Sai dai ya musanta zargin yana mai cewa babu kanshin gaskiya a cikinsa.

A cewar takardar shigar da kara da dan sanda mai gabatar da kara, Zakka Musa, ya mika wa kotun, ana zargin Aminu Yar’Adua da buge mutum shida yayin tukin ganganci a kan babban titin Yola.

Kotun ta ji cewa mutum hudu daga cikinsu sun mutu yayin da biyu suka samu raunuka, tana mai cewa mutanen sun fito ne daga yankin Sabon Pegi da ke Karamar Hukumar Yola Ta Kudu.

“Mutanen da suka mutu lokacin hatsarin su ne; Aisha Umar (mai shekara 30), Aisha Mamadu (mai shekara 32), Suleiman Abubakar(dan shekara biyu) da kuma Jummai Abubakar (mai shekara 30), yayin da kuma Rejoice Annu (mai shekara 28) da Hajara Aliyu (mai shekara 27) suka ji raunuka,” a cewar takardar shigar da kara.

Dan sanda mai shigar da kara ya shaida wa kotun cewa iyalan marigayiya Aisha Umar da Jummai Abubakar da kuma marigayi Suleiman Abubakar sun bukaci a biya su N15m a matsayin diyya.

Alkaliyar kotun, mai shari’a Jummai Ibrahim, ta ɗage sauraren karar zuwa ranar 19 ga watan Agustan 2021, inda ta bayar da umarni a kai Aminu Yar’Adua kurkuku kafin lokacin.

‘Ba dan Umaru Yar’Adua ba ne’

A bayanan da NAN ya bayar, ya ce Aminu Yar’Adua, ɗa ne ga marigayi shugaban kasa Umaru Yar’Adua.

Sai dai wata majiya daga iyalan tsohon shugaban kasar ta tabbatar wa BBC Hausa cewa ɗan marigayi Shehu Musa Yar’Adua, gwamnan mulkin soji na farko a Arewacin Najeriya ne.

Majiyar ta kara da cewa matashin ɗa ne ga Hajiya Binta, matar marigayi Shehu Yar’Adua.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here