Da Dumi-Dumi: Tsohon Ministan Noma, Alhaji Abba Sayyadi Ruma Ya rasu a Birnin Landan

INNALILLAHI WA’INA ILAIHI RAJI’UN Allah yayima Alhaji Abba Sayyadi Ruma rasuwa a yau bayan yayi fama da gajeruwar rashin lafiya.

Alhaji Abba Sayyadi ya rasu a wata asibiti ne dake a birnin Landan bayan ya ziyarci asibitin domin a duba lafiyarshi.

Abba Sayyadi Ruma wanda aka haifa a March 13, 1962 wanda ya rike mukamin sakataren Gwamnatin jihar Katsina kafin daga bisani ya zama Ministan Noma da kula da ruwan Nigeria a lokacin Mulkin Marigayi Ummaru Musa Yar’adua.

Allah ya jiqanshi da gafara yasa Aljanna ce makoma agareshi tare da daukacin yan’uwa musulmi da suka rigamu gidan gaskiya ameen, mu kuma Allah ya kyautata tamu bayan tasu idan ajalinmu yazo ameen.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here