INNALILLAHI WA’INA ILAIHI RAJI’UN

Tsohon Minista Kuma Shugaban Jami’ar Bayero Na Farko Mahmud Tukur Ya Rasu

Allah Ya yi wa tsohon Ministan Ciniki da Masana’atu, Dokta Mahmad Tukur rasuwa a safiyar Juma’a.

Dokta Mahmud Tukur, shi ne Shugaban Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) na farko, kuma makusanci ne ga Shugaba Muhammadu Buhari.

Iyalansa sun tabbatar wa Majiyarmu cewa ya rasu ne a Abuja bayan fama da rashin lafiyar da ta sa aka garzaya da shi zuwa asibiti daga Kaduna a ranar Alhamis da dare.

Za a kai gawarsa Yola, Jihar Adamawa domin yi masa jana’iza,” inji majiyar tamu
A lokacin rayuwarsa, Dokta Mahmud Tukur ya taba za darakta a kamfanin Cadbury Nigeria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here