INNALILLAHI WA’INA ILAIHI RAJI’UN

Tsohan Shugaban Hukumar Kula Da Ma’aikatan Jihar Katsina Ya Rasu Yana Da Shekaru 85

Allah ya yi wa tsohan Shugaban Hukumar Kula Da Ma’aikatan jihar Katsina, Alhaji Sani Katsina, wanda gogaggen maaikacin gwamnati ne, wanda ya yi aiki a wurare daban- daban, tun lokacin jihar Katsina na hade da jihar KADUNA, wanda ya yi ritaya tun a shekarar 1988. Bayan ya yi ritaya ne aka ba shi Shugaban Hukumar Kula Da Ma’aikatan jihar Katsina har sau biyu.

Alhaji Sani Katsina, ya rasu jiya litanin 7/12/2020 a gidansa, da ke cikin garin Katsina, kusa da gidan Marigayi Danmalikin Katsina, Alhaji Sada Ingawa, bayan fama da doguwar jinya, yana da shekaru tamanin da biyar da haihuwa. Ya rasu ya bar ‘yaya bakwai.

An yi Sallah jana’izar sa a gidansa da misalin karfe biyar na marecen ranar wanda Malam Tasi’u S. Kafur ya jogaranta. An kuma rufe shi a makabartar Gidan Dawa da ke cikin garin Katsina.

Cikin wadanda suka samu halartar jana’izar sa akwai mataimakin Gwamna jihar Katsina, Alhaji Mannir Yakubu da sakataren gwamnati jihar Katsina, Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa da Shugaban Ma’aikatan jihar Katsina, Alhaji Idris Tune da kuma manyan sakatarori da shugabanni maaikatu da sauran al’ummar gari.

Allah ya jikansa da rahama!

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here