TSARO: Zan Zagaye Jihar Katsina da Katanga idan na zama Gwamna….TATA

“Idan Allah ya bani dama na zama Gwamnan jihar Katsina nayi Al’kawarin kawo karshen wannan Shakiyancin na sace mutane” Inji Umar Abdullahi Tsauri TATA,

TATA yayi wannan Furucin ne a wajen Bikin Ƙaddamar da Shuwagabannin gudanarwa na yaƙin neman zaɓen sa a 2023 ƙarƙashin Inuwar Jam’iyyar APC a ɗakin taro na Katsina Motel dake cikin birnin Katsina.

Bayan Zayyano Duka Shuwagabannin tun daga matakin Jiha, yanki (Zones) da ƙananan Hukumomi, Umar Tata yaja hankalin su akan riƙe gaskiya da Amana, a haɗu ayi aiki tare saboda Allah,

Da yake Bayyana ƙudurin sa akan shawo kan matsalar Tsaro Umar Abdullahi TATA ya yi Alkawarin Daukar tsatstsauran Mataki, kuma a Shekarar sa ta farko, inda ya bayyana irin matakai da zai dauka.

“Na daga cikin Matakin Dauka, akan tsaro TATA ya bayyana cewa zai sanya a zagaye Yankunan iyakar Zamfara, Kaduna, zuwa Katsina, kuma zai Dauki ‘Yanbanga ɗari biyar a ko wane yanki da ake fama da Wannan ta’addanci, su zama cikakkun ma’aikata ya basu Bindiga saidai duk wanda zai ce, yace…Inji Umar Tata.” Taron da aka gudanar Ranar Lahadi 2/1/2022 wanda ya hada Dukkanin yankunan Jihar Katsina, daga nan aka dunguma zuwa wajen Bude Babban Ofishin Yakin neman Zaɓe da jin ƙorafe-ƙorafen Al’uma na Katsina, akan Titin Hanyar Kano kusa da Ofishin NEPA.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here