Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana cewa lokacin neman wanda ko wurin da za a dora laifin abinda ya jawo matsalar tsaro fa ya wuce. Abinda yake gaban mu yanzu, baki dayan mu, shi ne neman mafita.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yau, a Cibiyar bincike da ajiye kayan tarihi dake a Arewa House Kaduna, wajen bukin bude dakin karatu na cibiyar wanda tsohon Gwamnan Jihar Legas, kuma Jigon Jam’iyyar APC na kasa Sanata Ahmad Bola Tinubu ya gyara.

Alhaji Aminu Bello Masari ya kara da cewa tabbas akwai inda muka saki layi, ganin yadda mutanen da a da muke tare, kuma muke tafiyar da duk al’amurran mu tare, amma ga shi yau mun zama abokan gabar juna. Babban abin tashin hankalin ma shi ne ‘yan ta’addan nan a warwatse suke, basu da wani jagoranci kwara da suke bi, haka kuma babu wani abu daya tartibi da suka sa a gaba a zaman bukatar su ko dalili na kai hare hare, cin zarafi da kisan al’umma da suke yi a kullum.

Saboda haka, ya zama wajibi muyi karatun ta natsu kan wannan lamari, domin idan har ba a gano bakin zaren ba, to murkushe wutar wannan fitina ta mutu kurmus zai wahala.

Da ya juyo kan makasudin taron kuwa, Gwamna Aminu Bello Masari, wanda shi ne Babban Bako na Musamman a wajen wannan buki, ya yaba wa Sanata Bola Tinubu saboda wannan gagarumar gudummawa da yaba Jami’ar Ahmadu Bello ta gyaran wannan dakin karatu mai dadadden tarihi. A inda ya bayyana cewa aiki ne da ya kamata ace mu ‘yan Arewa munyi, musamman gwamnatocin jihohin Arewa, saboda mu maka fi kowa cin gajiyar Sardauna Ahmadu Bello.

Ya kuma yi godiya ga hukumar gudanarwa ta Jami’ar Ahmadu Bello domin wannan karamci da suka yi mashi zama Babban Bako na Musamman a wannan taro.

A cikin watan Fabrairu da ya gabata ne Sanata Bola Tinubu ya jagoranci taron lakcocin da akeyi duk shekara a Cibiyar domin tunawa da Firimiyan Arewa Alhaji (Sir) Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato. Kuma ganin halin da dakin karatun yake ciki yasa Sanata Tinubu yasha alwashin gyara shi, wanda ga shi yau an kammala har an bude.

Daga cikin manyan bakin da suka halarci wannan buki akwai Gwamna Nasiru El Rufa’i, wanda Kwamishinan Ilimi Dokta Shehu Muhammad Makarfi ya wakilta, akwai Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas da Mataimakin shi Dokta Kadiri Hamza ya wakilta. Akwai Alhaji Nuhu Rubadu, Dokta Kashim Imam, Mataimakin Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello Farfesa Kabiru Bala.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here