Gwamna Aminu Bello Masari yayi kira ga hukumomin tsaro dasu dauki tsauraran matakai na gaggawa domin kawarda jagororin ‘yan ta’adda, musamman masu fitowa suna gadara da kalaman izgilanci a kafafen sadarwa na zamani. Yin hakan zai dawo da martabar hukumomi da jami’an tsaron a idon al’umma sannan kuma zai sa’ yan ta’addan su shiga taitayin su domin yanzu suna ganin sun fi karfin kowa.

Gwamna Aminu Masari yayi wannan kiran ne yau a fadar Gwamnatin Jiha yayin da ya karbi bakuncin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Alhaji Usman Alkali Baba. Alhaji Aminu Bello Masari ya kuma shawarci Sufeto Janar din da ya bada karfi sosai wajen amfani da fasaha (Technology) wajen gudanar da aikin su na yaki da ta’addanci da sauran manyan laifuffukan da suka zame wa kasar nan karfen kafa.

Alhaji Aminu Bello Masari ya kuma bayyana cewa babu dalilin wani cece kuce a kan kiran da yayi na al’umma su kare kan su, domin kuwa shi yayi magana ne bisa ga fahimtar shi da al’amarin a matsayin shi na Gwamnan Jihar Katsina, su ma wadanda suke nuna rashin aminta da kiran nashi, suna yi ne a kan iya fahimtar su ta masu hangen al’amarin daga nesa.

Ya Jaddada cewa ba fa zai yiwuwa ba mutane suyi zaune ayi ta ci masu zarafi ana kisa ba tare da sun daga hannun kare kai ba, tare da bayyana cewa duk halitta dama can a dabi’a ita ke fara kare kanta daga hari kafin a kawo mata dauki.

Gwamna Masari ya kuma tabbatar da cewa Gwamnatin Jiha za taci gaba da ba hukumomi da jami’an tsaro duk irin gudummawar da take iyawa don ganin an murkushe ta’addanci da ‘yan ta’adda.

Tun farko a jawabin shi, Sufeto Janar Usman Alkali Baba ya shaida wa Gwamna Aminu Masari cewa yazo Jihar Katsina domin ya gani kuma yaji halin da ake a kan yaki da ta’addanci da ake tayi wanda yaki ci yaki cinyewa.

Ya kuma bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashin basu duk goyon bayan da suke bukata domin cin nasarar wannan yaki dama sauran ayyukan da rundunar ta ‘yan sandan Najeriya take yi.

Ya ce akwai sabbin tsare tsare da shirye shirye da suka fara shigo dasu domin canza salon yaki da ta’addanci wanda za su kai ga cin nasara.

Alhaji Usman Alkali ya kuma yi ga al’umma da kowa ya tashi tsaye ya bada gudummawar domin aikin samarwa tare da tabbatar da tsaro na kowa ne ba tare da nuna wani banbanci ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here