Advert
Home Sashen Hausa TSARO: Dokar kasuwannin sati a Katsina Mutane sunyi biyayya

TSARO: Dokar kasuwannin sati a Katsina Mutane sunyi biyayya

TSARO: Dokar kasuwannin sati a Katsina Mutane sunyi biyayya;

Zaharaddeen Mziag @Katsina City News

Al’hamis: 2/9/2021

Kasuwar Batsari kenan a Jihar Katsina Inda ‘yan Bindiga sukafi Addabamawa

Kamar yanda aka sani tsaro ya taɓarɓare a jihar Katsina inda akullum ba’a rasa kauyen da masu garkuwa da mutane suka kaima hari, su kashe ko su sace, hakan ya sanya Gwamnatin jihar Katsina a ƙarƙashin jagorancin Aminu Bello Masari, yasanya wasu Dokokin da ake ganin zasu kawo saukin yawaitar kashe-kashe da sace sace a yankunan jihar.

Daga cikin Dokokin da Gwamnatin ta sanya akwai taƙaita zirga-zirga, da rufe wasu daga cikin hanyoyi irinsu Jibiya zuwa Gurbi, da wani bangare na yankunan Dan’musa

Hana hawa Babur fiye da mutum biyu, rufe gidajen sayar da manfetur, a yankunan da abin yafi tsanani da kuma hana cin kasuwannin da matsalar tsaron tafi ƙamari, irin su Batsari, Gurbi, Mai adua, Matazu, Ɗanmusa

Da kuma hana yawon Dare, ga Al’umar jihar ta katsina bakiɗaya, inda Al’uma sukafi tofa al’barkacin bakinsu, wasu na ganin dokar tayi daidai, wasu kuma cewa suke, jami’an tsaro ne suka gaza bada gudummawar da ta dace,

Ko a makonnan da ya shige KATSINA CITY NEWS ta samo wani Faifain Bidiyo da ya nuna Danmajalisar Ɗanmusa yana tofin Allah tsine ga Shugaba Buhari akan gazawar Gwamnatin na samar da tsaro dukda a cewarsa, babu inda akafi bawa Buhari kuru’a akamr jihar Katsina amma ya gaza yin abinda ya dace, wanda idan akaso sati ɗaya an gama da Matsalar,

Ayayinda Shikuma Danmajalisar jiha mai wakiltar karamar hukumar Mani, yake cewa; Gwamnatin jihar katsina tana ware miliyoyin kuɗaɗe duk wata ana bawa kwamitin tsaro domin samar da dauwamammen zaman lafiya a jihar, amma kamar ana ƙara haddasa fitinar, wanda yayi kira da abinciki kwamitin tsaron kuma ayimasa garanbawul.

Ko a jiya dai a yankin zamfara me makwaftaka da katsina masu garkuwa da mutane sun sace ‘yan makaranta kusan ɗari da saba’in a wata majiyar domin neman kudin fansa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Shugaba Buhari ya nemi kasashen duniya su yafewa Najeriya bashin da suke binta

A yayin da yake gabatar da jawabi a zauren majalisar dinkin duniya a ranar Juma'a. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi manyan kasashen duniya...

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina Saifullahi Kuraye‎ September 24, 2021 2 min read Bangaren aikin jarida na...

Hukumar Hana Fasa ƙwabri ta ƙasa wato Custom ta ƙwato Babura Ɗari Biyu da Biyu a Jihar Katsina…

Shugaban Hukumar Ƙwastam na Jihar Katsina Mr. Chedi ne ya bayyana hakan ne a Yau Juma'a cewa tsakanin watan Agusta zuwa Satumba Hukumar ta...

Dan Najeriya ya fiye tsogwami: da ₦500 kacal sai aci a ƙoshi……Inji farfesa Segun Ajibola

Da Naira Dari Biyar ( 500 ) kacal Zaka Iyaci Ka Koshi a Najeriya, Cewar Wani Farfesa, Masanin Tattalin arziki... Tsohon shugaban kwalejin ma'aikatan bankin...

Rail project will not displace host communities-FG

Radio Nigeria The Federal Ministry of Transport and that of Environment have given assurance to residents along the proposed stretch of land demarcated for the...
%d bloggers like this: