Advert
Home Sashen Hausa TSAKANINA DA GWAMNATIN KATSINA(kashi na uku)

TSAKANINA DA GWAMNATIN KATSINA(kashi na uku)

 

Kabir sadiq (Dan Abu)

A baya na tsaya inda mukayi waya da ADC kuma yaje ya gaya wa maigirma gwamna yadda abun yake, shi Bafarawa akai ta nemansa ya kulle wayoyinsa duka. Daga karshe dai wurin police na kwana.

Da asuba nayi sallah sai na amshi wayar wani police na kira iyalina, a lokacin ana ta maganar an sace ni. Daga nan surikina ya.kirawo kanensa lokachin AIG ne, shikuma yakira CP na Katsina. Ba’ayi awa guda ba a kazo akace in fito, wasu police muka zanna da su wani office suna ta bani hakuri cewar sun san abin nan duka siyasa ce kada in damu, suka gama bayanan su suka bani wayoyina da makullin mota ta, suka sallameni.

Bayan gwamna ya dawo daga Abuja naje nayi masa bayani da kaina, yayi shiru kawai yana shafa fuskar shi. Ya gwada damuwarsa kiri-kiri. Nan dai ya bani hakuri kuma yayi mani wasu nasihohi masu nuni da hakuri ga wanda aka zalunta koda kuwa yana da ikon ramawa, karshe alkhairi ne zai biyo baya. Muka gama mu kayi sallama.

To shi kuma zonal director watau Abdulaziz Kukasheka sai suka sa police suka kamoshi, Akwai Fc na ministry for local government Alh. Shitu Kurfi da director works Abubakar ‘Yargoje suka hana a wulakanta wannan bawan Allah domin sun hango abinda ka iya zuwa ya dawo ba zai yi kyau ba. Amma duk da haka mutumen nan sai da aka rabashi da wurin aikinsa inda yake kula da kananan hukumomi 5 -Malumfashi da Kankara, da Kafur da Bakori da kuna Danja. Aka jingine shi sama da shekara guda baya da wurin aiki.

Lokaci-lokaci muna magana da shi, har Allah yasa aka dawo tenure ta biyu, cikin ikon Allah akabi hanyoyi muka samu aka maida shi bisa matsayinsa na zonal inspector mai kula da -Funtua da Fasakari da Dandume da Sabuwa da kuma Bakori. Wanda yanzu haka yana bisa aikinsa.

Anci gaba da hidima amma makirce-makirce sai kara gaba suke yi.

Alhamdulillahi maganar da maigirma gwamna yai mani ta muhimmancin hakuri sai gashi ba a yi shekara daya ba Allah ya tarwatsa tsakanin Zakka da SGS. Domin mun je 2019 campaign a Safana kuma duk masu bayani sun yi bayani ana ta tafi da jin dadi.

Amma da SGS ya hau podium Wallahi sai wuri ya rude da ihu da jifa da zagi kala-kala. Wallahi tun da nake duniya ban taba ganin wanda aka cima mutunchi haka ba. Kuma mutanen mazabarsa ne ta Safana, Danmusa, Batsari. Sai da maigirma gwamna ya hau ya fara magana sannan mutane suka bar zagin SGS. Kuma lokacin da muke tashi taro Wallahi idan da bai shiga motar gwamna ba da wuya ya dawo gida lafiya.

Bayan an dawo sai akace Zakka ne ya sanya aka yiwa SGS wannan wulakancin da cin mutunci. Daga nan aka daura zare.

An dawo second tenure Zakka da ke commissioner na ministry for local government and chieftaincy affairs ya koma commissioner for special duties, a shekara guda baya ganin 50,000 ta gitta gabanshi.

Shi kuma SGS gashi nan yau Abdullahi Taliya ya fi shi kwanciyar hankali.

Kuma maganar liabilities da akai tayi mani kafar angulu na kada a biya, bayan na fita sabgar gaba daya na bar zuwa gidan gwamnatin kwata-kwata, gwamna yasa aka yi bincike kan kudin kuma aka tabbatar da gaskiya, kuma yasa aka biyani kudina gaba daya.

Maganar kujeru kuma bayan na bar hidimar, na bar zuwa gidan gwamnatin gaba daya Alhaji Muntari Lawal yasa aka kira Ciyaman na Subeb yace masa akwai kenensa Alhaji Kabir yana da kujeru daya kawo daga China, idan akwai bukata yanason su sayesu. Yayi mani magana yace inje inga Ciyaman na Subeb. Suka fara sayen na 18m daga baya suka sake sayen a 31m. Alhamdulillahi.

Allah yana son masu yafiya.
Wata rana wani amini na Alh. Haruna Goshi ya kirawo ni ta waya yace mani gashi nan tare da Zakka kuma Zakka yace don Allah ya rokeni in yafe masa abinda yayi mani yace Wallahi duk abinda yayi mani SGS ya sanya shi. Ya bani Zakka muka yi waya da shi yace ma ni Alhaji Kabir don Allah kayafe mani abubuwan da nayi maka yace Wallahi nayi nadama kwarai da gaske. Nayi shiru Ina tuna abubuwan da suka faru baya, da yaji nayi shiru sai yaba Abdulhadi Babban Duhu wayar shima yaci gaba da bani hakuri, daga karshe nace yaba Zakka wayar, ya bashi waya nace masa Abdulkadir Zakka duk abinda kayi mani na yafe maka, kuma ina rokon Allah ya yafe mamu kurakuran mu gaba daya. Wallahi ina jin shi yana shashshekar alamar kuka, nace masa kada ya damu.

Bayan ‘yan kwanaki ya kirani ta waya yace mani kabamu lokachi inzo inkara baka hakuri, nace masa ai magana ta wuce yache a a shi dole sai yazo. Suka zo washe gari shida Haruna suka same ni gidana muka wuni muna tantaunawa. Muka yi hotuna tare kana mukayi sallama.

Ko satin daya wuce Zakka ya kawo mani ziyara gidana nan muka wuni da shi da wasu abokanansa.

Cikin hidimar nan na zubar da hawaye sau ukku. Na farko mamaki ne yasa na zubar da hawaye, na biyu tausayi ne yasa na zubar da hawaye, na ukku kuma ganin girman Allah na yadda yake maida sarki ya koma talakka shi ne ya sanyani hawaye.

Na farko zuwana wajen Yansanda da yadda akaci mani mutuncina babu gaira babu dalili.

Na biyu yadda naje na gaya wa gwamna abinda akayi mani, gashi kiri-kiri ya gwada damuwarsa amma abin yafi karfinsa. Wallahi saboda tausayin halin da naga ya shiga sai da na zubda hawaye.

Zubda hawayena na ukku shi ne zuwan da Zakka yayi gidana last week, naga mutumen da saboda madafun iko da kudi dake hannunsa na 34 local governments yaci mutuncina ba a shekara ukku ba gashi yau cikin gidana baya iya maganin dubu goma, Wallahi saida na zubar da hawaye. Kuma na kara imani da cewar Allah shi ne mai iko akan kome.
Mun kawo karshen rubutun Dan abu da muka dauko daga shafin sa na Facebook

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

WATA SABUWA: Kotu a jihar Gombe ta ci saurayi tarar Miliyan 2.6 saboda yaki auren budurwar sa

Daga: Yushau Garba Shanga Wata kotun majistiret da ke da zama a Kumo fadar ƙaramar hukumar Akko a jihar Gombe ta yanke wa wani matashi...

Rundunar Yansanda Ta Jihar Katsina Ta Chafke Daya Daga Cikin Yan Bindiga Da Suka Hallaka Hakimin Yantumaki.

Rundunar Yansanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar chafke daya daga cikin Yan Bindiga da suka hallaka Tsohon Hakimin Yantumaki Marigayi Abubakar Atiku Maidabino,mai...

THE DUALIZATION OF THE IBADAN – ILORIN EXPRESSWAY AND SECTION II OF THE OYO – OGBOMOSO ROAD BY THE BUHARI ADMINISTRATION IS ALMOST DONE!

#PositiveFactsNG In staying true to its passionate commitment to developing Nigeria's infrastructure, do you know that the dualization of the Ibadan - Ilorin Expressway as...

THE APAPA – OSHODI – OWORONSHOKI EXPRESSWAY IS SET FOR COMPLETION AND COMMISSIONING!

https://www.facebook.com/Do-You-Know-NG-101788642037662/ THE APAPA - OSHODI - OWORONSHOKI EXPRESSWAY IS SET FOR COMPLETION AND COMMISSIONING! #PositiveFactsNG Do you know that the reconstruction project of the Apapa - Oshodi...

Kungiyar Mafarauta ta Najeriya HCN ta Karrama Mataimakiyar shugaba ta ƙasa

Kungiyar Mafarauta ta Najeriya HCN ta Karrama Mataimakiyar shugaba ta ƙasa Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News 6/12/2021 Kungiyar Mafarauta ta Najeriya, wato Hunters Council of...