Advert
Home Sashen Hausa TSAKANINA DA GWAMNATIN KATSINA ( kashi na biyu)

TSAKANINA DA GWAMNATIN KATSINA ( kashi na biyu)

Daga kabir sadiq ( dan abu)

A cikin bayanina na baya, na fadi yadda maigirma gwamna ya damka maganar koken dana kai masa a hannun SGS don yabi kadin maganar liabilities dina dake hannun commissioner na kananan hukumomi, to na yi ta zuwa wajensa, wani lokachin yace mani bai ga commissioner na local government ba watau Abdulkadir Zakka, wani lokacin yace mani sun yi magana zai zo ya same shi, haka akai tayi har tsawon wata hudu.

Wata rana na yanke shawarar in je ministry for local government and chieftaincy affairs domi in bincika maganar nan. Naje wajen permanent secretary Dandauda domin Inji ko maganar tazo wajensa, inda yace mani gaskiya bai san da maganar ba.

Daga nan na wuce wajen director works Abubakar ‘Yargoje abokin yayana ne. Nayi masa bayanin abinda yakawo ni, yace eh, ga file din nan gabansa, nace masa wannan instruction na maigirma gwamna ya kai wata biyar amma har yanzu ba’ayi wani abu ba. Nace masa ya kamata kayima commissioner magana shi sha’anin aiki in yazo yinsa ake yi koda kuwa akwai wani abu personal tsakani.

Sai yace mani “Wallahi ķanena bani da sufanun da zan iya gyara commissioner, amma kayi hakuri zan san yadda zan yi”. Mu kayi bankwana na tafi.

Bayan wata guda sai wani ya gaya mani an kawo report na aikina daga Danja local government, naje ministry na kasa samun wani bayani game da maganar.

Sai na nemi lambar zonal inspector mai kula da Funtua zone sunanshi Abdulaziz Kukasheka, mu kayi magana da shi yace mani ai ya kawo report akan aikina. Nace masa naje ministry amma ance ba a kawo report ba. Mu kai ta magana daga karshe na nemi ya taimaka ya bani copy na report din, bayan na amsa sai na kira Nasiru Babban duhu wanda tare yake da Zakka, muka hadu nace masa ya kamata ka gayawa Zakka ba’a personalizing aikin gwamnati, kuma na gwada ma shi takarda nace kaga report wanda aka kawo kan aiki na amma an ki kaima gwamna.

Nan ya.gwada rashin jin dadin sa kuma yace zaije ya samu Zakka.

Daga nan shi Nasuru bai kara nemana ba, sai kawai wata rana wani ya.kirani cewar kaine Alhaji Kabir Sadiq? Nace masa eh, sai yace toh kana Katsina? Nace masa eh, sai.yace to Don Allah kazo nan police headquarters bangaren SIB ka nemi Sabi’u munamson ganinka.

Na dauki mota sai police headquarters. Na samesu muka gaisa, sai suka kaini wajen ogansu ana ce mashi Bafarawa. Bayan mun gaisa sai yace mani Alhaji an kawo koke a kanka kaje ofishin Zakka kache zaka kashe shi da shi da director works Abubakar ‘Yargoje.

Nace masa ban san wannan maganar ba sai yanzu. Ya dauko petition da aka rubuta akai na ya bani na karanta, ina dubawa sai naga daga chamber wani lauya ne mutumen SGS aka rubuto koken.

A takardar an gwada mutane biyu ne su kayi koken Abdulkadir Zakka da Abubakar ‘Yargoje watau director works. Na gama karantawa, nace musu wannan maganar yanzu na fara jinta. Nan take na kira Director works Abubakar ‘Yargoje nace masa gani nan police headquarters an kira ni kan koken da kuka rubuta kai da Zakka wai nace zan kashe ku. Sai yace mani kanena ni babu ruwana da wannan maganar, kuma bani na rubuta takardar nan ba kuma bansan wanda ya rubuta taba.

Nima an kirani inzo in bada statement, kuma lokacin ne naga takardar karon farko.

Kuma kace su baka statement wanda na rubuta ka gani, na rubuta bansan da wannan takardar ba. Kuma yace mani a takarda an
rubuta Engineer Abubakar ‘Yargoje, yace kuma shi ba Engineer bane shi quantity surveyor ne. Saboda haka shi wallahi babu ruwanshi.

Duk wannan maganar wayata tana speaker aka yita gaban ‘yansanda. Na rubuta statement suka ce to in tafi amma gobe in dawo karfe 10 na safe.

Wan shekare aka tashi da ruwan sama, har karfe 11, na kirasu nace toh gashi kun ce inzo 10 kuma gashi ana ta ruwa. Sukace babu kome idan an gama ruwan sai kazo.

Wajen karfe 3 naje, sai shi Bafarawa yace Alhaji akwai wata takarda wajenka wadda zonal director yabaka? Nace eh, yace tana ina nace tana gida, yace to suna son in kawota. Suka hadani da wani police mukaje na dauko takardar, daganan sai suka kirawo Zakka da shi da Nasuru Babban Duhu, muka fara bayani daga nan muka fara rigima da Zakka, abu yayi zafi na tashi zan buge shi, aka shiga tsakani aka rirrike ni, sai akace ni in koma office din 2ic in zauna.

Ina wurin har la’asar, mukayi salla muka dawo. Ina wurin har karfe biyar, sai kawai wani yazo yace ance in bada wayoyina. Nace saboda me? Yace Alhaji kayi hakuri kai mutum ne mai mutunci kuma duk mun fahimchi abin nan Wallahi babu yadda zamuyi ne. Daga karshe na bashi wayoyina duka.

Ina wurin har magariba, mukayi sallah, daga masallaci wani police yace mani Alhaji oga yace mu tsare ka. Nace tsarewa? Yace eh, nace masa toh wannan yayi kama da kidnapping, an kirawoni babu wanda yasan inda nike a yanzu fa. Wallahi yaron nan yabani wayarsa na kira iyalina har sau biyar ba a dauka ba. Chan sai natuna ina da wayar wani SS na gwamna a kaina. Sai na kirashi suna Abuja nace masa yabgaya ma gwamna su Zakka sun kawoni wajen police wai nace zan kashe su.

Bayan Dan lokachi sai ga S.O. yazo wajen yace mani ADC Lawal Joka ya kirawo shi daga Abuja yace yazo police headquarters gwamna yace in gayawa ADC abin dake faruwa. Aka kirawo ADC mukayi magana nagaya masa duk abinda ke faruwa. Kuma ya gayawa gwamna.

Zanci gaba daga nan in sha Allahu.kashi na uku.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE BUHARI ADMINISTRATION SUPPORTS THE LAGOS STATE RAILWAY PROJECT!

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/232549375628254/

Kotu ta rushe shugabacin jam’iyar APC ɓangaren Ministan Ilimi, Adamu Adamu a Bauchi

Babbar kotu a Jihar Bauchi ta rushe shugabacin Babayo Ali Misau na jam'iyar APC a jihar. Rahotanni sun baiyana cewa shi dai Misau yaron Ministan...

2023: Don’t Allow Politicians to Use You, Atiku Group Tells Youths

2023: Don’t Allow Politicians to Use You, Atiku Group Tells Youths editorDecember 5, 2021 4:50 Pm Francis Sardauna in Katsina Ahead of the 2023 general election, the...

‘Yan Bindiga Sun Tsananta Kai Hare-hare Akan Hanyar Gusau Zuwa Shinkafi

Daga Dauda Umar Januhu 'Yan Bindiga a jihar Zamfara suna cigaba da kai zafafan hare-hare tare da sace mutane akan babbar hanyar da ta tashi...

DSS sun kama Janar Dambazau a Kano…

DSS sun kama Janar Dambazau a Kano Jami'an Ƴan sandan Farin Kaya, DSS sun kama Janar Idris Dambazau, Shugaban Hukumar Kare Haƙƙin mai Sayan Kaya...