Tsadar Albasa ta tabbatar da halin matsin da Najeriya take ciki- Sarkin musulmi Sa’ad Abubakar

Tsadar Albasa ya nuna tsananin matsin da ƙasar nan take ciki, inji Sarkin musulmi Sa'ad Abubakar

Tsadar albasa ta tabbatar da wahalar da ake ciki a Najeriya – Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi Abubakar Sa’ad III ya yi bayani kan matsalolin tsaro da tattalin arziki da Najeriya ke fama da su.

Da yake jawabi a wajen taron majalisar shugabannin addinai ta Najeriya, Sarkin Musulmin ya bayyana girman matsalar tsaro inda ya ce “yanzu ƴan fashi har cikin gida suke zuwa su garkuwa da mutane,” kamar yadda Shafin Twitter na Majalisar ƙoli ta harakokin addinin musulunci ya bayyana.

Sarkin Musulmin kuma ya ce yadda albasa ta yi tsada ya tabbatar da girman wahalar tattalin arzikin da ake ciki a yanzu a Najeriya.

Social embed from twitter

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here