Trump ya so ya kai wa tashar nukiliyar Iran hari

Jaridar New York Times ta ruwaito cewa mashawartan Shugaba Trump sun gargaɗe shi a makon da ya gabata da kar ya kai hari kan tashar nukiliyar Iran.
An ruwaito cewa Trump ya nemi shawarar babban mai ba shi shawara kan harkar tsaro game da yiwuwar kai wa Iran hari ranar Alhamis da ta gabata.
Sai dai daga baya Trump ya canza ra’ayi bisa tsoron abin da hakan zai haifar a Gabas ta Tsakiya.
New York Times ta ce shugaban ya fara neman shawarar ne bayan wani rahoton hukumar kula da makaman nukiliya ta IAEA ya bayyana cewa Iran na ci gaba da inganta makamashin uranium, wanda ake haɗa nukiliya da shi.
Ana tunanin harin zai faɗa ne kan tashar Natanz, wurin da IAEA ta ce “uranium ɗin Iran ya ninka sau 12 na wanda aka amince mata a ƙarƙashin yarjejeniyar da Trump ya cire Amurka daga ciki wadda aka ƙulla a 2018”.
Kawo yanzu babu wani martani kan rahoton daga Fadar White House.