Trump ya ruga kotu yayin da Biden ke kan hanhyar samun nasara

Trump ya ruga kotu yayin da Biden ke kan hanhyar samun nasara

Trump ya ruga kotu yayin da Biden ke kan hanhyar samun nasara

Donald Trump

Donald Trump da abokin hamayyarsa ta Democrats, Joe Biden kowanne su ya gabatar da jawabi ga Amurkawa yayin da hankula suka karkata kan sauran jihohin da yanzu ake fafatawa dan kammala sanin sakamakon zaben.

Mista Trump ya sake korafin magudin zabe, ba tare da bayyana wasu shaidu ko hujja ba.

A wani jawabin daya gabatar a Fadar white House, ya yi korafi cewa an sace kuri’unsu ta haramtattun kuri’u.

A jihohin Pennsylvania da Georgia, Trump nasararsa ta soma tangal-tangal bayan soma kidaya kuri’un da aka kada ta akwatin gidan waya.

Shi kuwa abokin hamayyarsa, Joe Biden ya dage kan cewa komai na tafiya daidai a kidayar.

A wani sakon talabajin dan takarar ta Democrats ya bukaci a kwantar da hankula da sake haƙuri.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here