Bayanin aikin hanyar da za ayi wadda ta tashi daga Jibiyar Maje dake karamar hukumar Jibiya zuwa Tashar Aibo ta jihar Maradin Jamhuriyyar Nijar.

A cikin watan Satumba na shekarar da ta gabata Gwamnan Jihar Maradi Alhaji Zakari Oumarou, bisa umurnin Shugaba Mahamadou Issoufu na Jamhuriyyar Nijar, ya kawo ma Gwamna Aminu Bello Masari ziyara ta musamman domin a roki Gwamnatin Jiha ta gina wannan hanya mai tsawon kilomita ukku domin ta hadu da hanyar da suka gina sabuwa daga Maradi zuwa Madarunfa.

Gina wannan hanya zai saukaka hanyar sufuri da bunkasa tattalin arzikin jihohin biyu.

Wannan aikin hanya, aiki ne wanda za ayi bisa ga tsarin ayyukan Gwamnatin Tarayya, kuma hanya ce ‘yar lumuilumui (dallof), kuma saboda yanayin kasar wurin da kuma yawan motocin da ake sa ran suyi zirga zirga kan ta, za ayi amfani da garin dutsi ne wajen yin daben hanyar madadin jar kasa mai danko da aka saba gani.

Akwai kuma wurin da rafi ya gitta kuma za a gina gada a wurin mai tsawon mita sittin (60m) da kuma fadin mita goma sha biyar (15m).

Akwai kuma hanyoyin ruwa da kwalbatoci da aikin ya kumsa.

Wannan hanya dai ta kasa da kasa ce, amma Gwamnatin Tarayya ta yarjewa Gwamnatin Jiha ta gina ta da amincewar za ta maida mata kudinta cif bayan kammala aikin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here