Advert
Home Sashen Hausa TIRKASHI: Yan sandan Katsina sun cafke wasu tubabbun Yan ta'addan da suke...

TIRKASHI: Yan sandan Katsina sun cafke wasu tubabbun Yan ta’addan da suke sojan gona

 

Hassan Male Kankara

@ katsina city news

Rundunar Yansandan Jahar Katsina ta samu nasarar kama wasu rukakkun masu satar shanu, gami da kwato shanu guda biyu da suka sace.

Kakakin Rundunar Yansanda na Jahar SP Gambo Isah ya gabatar da masu laifin ga Manema Labaru a madadin Kwamishinan Yansandan Jahar CP Sanusi Buba.

Acewar SP Gambo Isah, a kokarin da Rundunar take yi na magance ta’addanci da masu aikatashi a Jahar, ta samu nasarar kama wasu masu laifi daban-daban da suka hada da; Tubabbun Yan bindiga dadi Wanda suke bayyana kansu a matsayin Manyan Jami’an Gwamnati tare da aikata Fashi da Makami da sace Shanu, da Kuma da masu Garkuwa da mutane da sauran Yan ta’adda.

Kakakin Rundunar Yansandan ya bayyana cewa biyo samun bayanan sirri, Jami’an Rundunar da aka hada da ‘Operation Sharan Daji’ sun kama wani Muntari Yusuf Mai shekaru 40 dake Kauyen Lugge, Wanda ya kasance rikakken barawon Shanu ne dauke shanu guda 3 na sata.

SP Gambo Isah yace a yayin gudanar da bincike ya tabbatar dacewa, Yana aiki da wata tawagar wani Kasurgumin barawo Mai suna Sani Muhudinge dake Daji, inda ya tura shi ya kai shanun ga wani Mallam Bello a Kauyen Dan Bafashi domin sayarwa a Kasuwar Runka.

Ya kara dacewa, Muhudinge ya kasance sau hudu yana turashi sayar da shanun a Kasuwar Gusami ta Jahar Zamfara.

Kakakin Rundunar Yansandan yace, Rundunar Yansandan ta kama wani tubabbun Yan ta’adda da suka hada da Abdullahi Mai-Rafi Mai Shekaru 43 dake Kofar Marusa, da Kuma Abbas Haruna da akafi sani da Dogo-Abbas dake Filin Polo, da Usman Hassan wanda akafi sani da Manu a Kauyen Ganuwa ta Karamar Hukumar Charanchi, wanda sukace suna aikin hadin gwuiwa da Gwamnatin Jaha da Hukumomin tsaro.

“Wadannan Yan ta’adda sunje da wata mota kirar Camry gami da farmakar wani Makiyaye Alhaji Gide Sulaiman, dake Karamar Hukumar Malumfashi a lokacin da yake kiwo, inda suka ce daga Ofishin Mai baiwa Gwamna Shawara na Musamman akan tsaro, tare da tuhumar karya cewa wani yaronsa Sa’idu ya yiwa wani Lawal Fashin shanu, Kuma sai ya fito dashi ko ya biya Shanu 100”

“Bayan an cigaba da tattaunawa, sun samu nasarar tafiya da shanu 20 na Alhaji Gide Sulaiman da darajar su takai Naira Miliyan 7, 550, 000:00 da manufar daukar diyya akan Shanun da yaron shi ya sata. Sun kuma cuce shi Naira Dubu 40,000:00 da tafiya da wayoyi 4 bayan sun duba jikin shi” Inji SP Gambo Isah

Kakakin Rundunar ya kara dacewa, sun kuma taba dawo wa domin kara cutar shi wasu shanun, amma sai yayi saurin sanar da Yansanda, inda aka kamasu, tare da gano shanu guda biyu da suka saida a matsayin shaida.

“Daya daga cikin Yan ta’addan Abdullahi Mai-Rafi ya kasance Kasurgumin Dan ta’adda ne amma ya tuba, inda a yanzu yana aiki da Gwamnatin Jaha Karkashin ofishin Mai baiwa Gwamna Shawara akan tsaro”inji Kakakin Rundunar Yansanda

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

NAF begins inquiry into alleged killings of civilians by Airforce pilot

The Nigerian Airforce has begun investigations into the alleged killing of civilians in Kamadougou Yobe State by an Airforce pilot. In a statement on Friday...

Yanzu haka cikin daren nan ‘yan bindiga sun afkawa garin Tangaza

LABARAI DA DUMI-DUMIN SU! Yanzu haka cikin daren nan 'yan bindiga sun afkawa garin Tangaza Labarai da muke samu sun tabbatar da cewa yanzu haka cikin...

Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso

Siyasa: PDP tayi watsi da tsagin Aminu Wali ta rungumi Kwankwaso Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta sanya ranar gudanar da zaben sabbin shugabanninta na...

Abdulaziz Ganduje ya kai karar mahaifiyarsa Gwaggo EFCC kan batun almundahana

Babban dan Gwamnan Kano, Abdulaziz Ganduje ya maka mahaifiyarsa Hafsat Ganduje gaban hukumar yakibda yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC akan zargin da...

Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina

Barawon Motar Gwamnati Ya Shiga Hannu A Katsina. Rundunar Yan Sanda ta Jihar Katsina ta samu nasarar chafke wani mai suna Hayatu Bishir da ake...
%d bloggers like this: