Tawagar ofishin mai bawa Gwamnan katsina shawara kan ilimi mai zurfi yakai ziyara a jami’ar umaru musa ƴar’adua.

Mai bawa Gwamnan katsina shawara akan Ilimi mai zurfi sunkai ziyara a jami'ar Umaru Musa Yar'adua.

Bashir Usman Ruwan Godiya mai bawa Gwamnan katsina shawara akan Ilimi mai zurfi

Ofishin Mai Baiwa Gwamnan Jihar Katsina shawara akan Ilimi Mai zurfi ya kai ziyara a jami’ar Umaru Musa Yar’adua (UMYU) dake Nan Katsina, Domin ganin irin matakan da jami’ar ta dauka da Kuma shirye shirye da take yi. Na dawowar dalibai don daukar matakan kariya na dakile Yaduwar cutar Corona Virus (Covid-19).

Mai Baiwa Gwamnan shawara Dr, Bashir Usman Ruwan Godiya ya zauna da Shugaban jami’ar Prof, Sunusi Mammam tare da sauran shuwagabinin gudanarwa na jami’ar.

Da yake gabatar da jawabinsa, Shugaban jami’ar ya bayyana irin matakan da jami’ar ta dauka tun daga farkon shigowa cikinta. Inda ya tabbatar Masa da cewa babu Wani mutum wanda zai shigo cikin makarantar ba tare da takunkumin fuska ba (face mask). Sa’an nan kuma sai an auna yanayin jikansa domin tabbatar da yadda yake.

Ya cigaba da cewa akwai ababen wanke hannu da aka girke a wajaje daban daban a cikin makarantar. Sannan a azuzuwan dalibai an dauki matakan tazara tsakanin mutum da mutum, kuma ya zama wajibi ga kowane dalibi yayi amfani da takunkumin fuska a lokacin da ya ke daukar darasi.

Shi ma a nasa jawabin Mai baiwa Gwamna shawara ya ce ya gamsu da wannan matakai da aka dauka domin ganin an kara dakile yaduwar wannan cuta data addabi Duniya.

Shi ma a nasa jawabin Shugaban kwamitin dake yaki da wannan cuta kuma Kwamishinan ma’aikatar yada labarai da al’adu ta jihar Katsina Hon. Abdulkareem Yahaya Sirika ya ce na shaida tun daga bakin kofar shigowa makarantar sai da aka tantance ni kanan na shigo. Shi ma ya yaba da matakan da jami’ar ta dauka.

Daga karshe Mai Baiwa gwamnan shawara tare da sauran masu ruwa da tsaki sun shiga cikin makarantar domin duba halin da makarantar take ciki da Kuma gane ma idanunsu abin da aka shaida masu.

Abdurashid Musa
Camera Man/Reporter
Mobile Media Crew
October 15/2020.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here