Advert
Home Sashen Hausa Tattabarar da aka sayar naira miliyan 893

Tattabarar da aka sayar naira miliyan 893

Tattabarar da aka sayar naira miliyan 893

New Kim

Wata tattabara da aka yi gwanjonta a Belgium ta kafa tarihi bayan da aka saye ta a kan dala miliyan daya da dubu dari tara, kwatankwacin naira miliyan 893 ke nan.

Tattabarar mai suna New Kim, ‘yar kimanin shekaru biyu da haihuwa macece, wanda kuma tun a farko aka sanya gwanjonta a kan fam 200, amma kuma sai aka samu wanda ya saye ta a kan makudan kudin da ya kai naira miliyan 893.

Kurt Van de Wouwer, shi ne mutumin da iyalansa suka raini wannan tattabara, ya ce sun kadu da suka samu wannan labari, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Mutumin da ya samu sa’ar sayen tattabarar da aka yi gwanjon nata Champion Racer Armando, ana masa lakabi da “Lewis Hamilton na tattabaru”.

Mutumin ya kasance yana kiwon tsuntsaye kala-kala da ya ke mai sha’awar kiwon ne.

Tattabarar wato New Kim, ta samu nasarar samun lambobin yabo da dama a wasu gasa da aka yi a 2018.

Yawancin tattarabarun da ke shiga gasar tsere na da farin jini kuma za su iya hayayyafa har zuwa tsawon wani lokaci, kuma ana kyautata tsammanin mutumin da ya saye ta zai yi amfani da ita ne wajen saka masa kwai.

Wadanda suka sanya gwanjon tattabarar sun ce wannan gwanjo ba a taba samun irinsa ba.

Sun ce farashin da aka sayi tattabarar ne ya kara armashin gwanjon da aka yi kuma abin mamaki ne ace an sayi tattabara mace a kan wannan tsabar kudi.

Bayanai sun nuna cewa akwai tattabaru da dama a Belgium kuma a wasu lokuta a akan yi amfani da su wajen samu kwai don a samar da irinsu da dama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Babu wanda zai bar jami’a saboda bai biya kuɗin makaranta ba -Farfesa Muhamad Sani Tanko

Babu wanda zai bar jami'a saboda bai biya kuɗin makaranta ba – Farfesa Muhammad Sani Tanko, Shugaban Jami’ar Jihar Kaduna ya kawar da tsoron da iyayen...

Police Arrest 60-Year-Old Man Conveying Rifles In Car Bonnet

A 60-year-old man, Umar Muhammed, was arrested while conveying firearms across the country. The suspect uses his vehicle to transport rifles concealed in the bonnet...

TABBAS ZA AYI ZABEN SHUGABANNIN APC …inji bagudu

TABBAS ZA AYI ZABEN SHUGABANNIN APC ...inji bagudu @katsina city news Gwamnan jahar kebbi bagudu ya tabbatar ma da Manema labarai a Abuja cewa tabbas za...
%d bloggers like this: