Taron Tunawa da Malam Umaru Musa ‘Yar’adua a Katsina:

Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina City News

Yau ne 5/5 shekara ta dubu biyu da Ashirin da daya, tayi dai-dai da cikar Shugaban kasar Najeriya malam Umaru Musa ‘yar’adua shekaru goma sha daya da Rasuwa.

Hajiya Habi Musa ‘Yar’adua

Jam’iyyar PDP a katsina karkashin jagorancin Hon. Salisu Yusuf Majigiri gami da ‘yan uwa da masoya sun shirya taron addu’a gami da fadar ayyukan alheri da yayiwa jihar katsina da ma kasa baki daya, a matsayinsa na Shugaban kasa na kusan shekaru ukku. Taron ya gudana a Sakatariyar jam’iyyar PDP dake cikin garin Katsina

Dayake jawabi a wajen taron bayan gudanar da addu’o,i Hon. Salisu Yusuf Majigir ya zayyano wasu muhimman ayyuka da marigayin yayi wanda har yau ake cin moriyar ayyukan da kuma kokarin da yayi na samar da tsaro a yankin Neja-Dalta wanda yace a halin yanzu bisa kokari na Malam Umaru musa yankin yafi katsina zaman lafiya saboda tasirin jajircewar Matawalle Umaru.

Idan muka dawo jihar katsina kuma shine Gwamna na farko da ya fara gina abinda ba za a taba mantawa dashi ba, inji Hon. Salisu Majigiri, inda ya bada misali da Sakatariyar Gwamnatin jiha, Filin jirgin sama, Jami’ar Umaru musa, da Babbar Asibitin Turai duk acikin Birnin na katsina banda manyan tituna da gidaje domin fadada jihar.

Hajiya Habi Musa ‘yar adua itace ta wakilci iyalai da dangi na Malam Umaru musa inda ta zayyano wasu daga cikin Halayen dan’uwan nata, irin su hakuri da cika Al’kawari, kuma tayi godiya a madadin mahaifiyar su Hajiya Da-Da, da sauran ‘yan uwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here