Advert
Home Uncategorized TARON SHIYYOYI NA ƘUNGIYAR MOPPAN A KATSINA YA ƘAYATAR

TARON SHIYYOYI NA ƘUNGIYAR MOPPAN A KATSINA YA ƘAYATAR

Zaharaddeen Mziag @Katsina City News

Comrade Lawal Rabe Lemoo MOPPAN Chairman

Haɗaɗɗiyar Kungiyar Harkar Fina-finai ta ƙasa reshen jihar Katsina sun gudanar da Babban taronsu na Shiyya da suke gudanar wa duk bayan watanni huɗu;

taron wanda ake kasashi uku,. shiyoyin Katsina Funtua da Daura, Inda a watannin baya aka gudanar da tarukan a yankin Funtua da Daura, a wannan wata na Agusta kuma takwas ga wata, an gudanar dashi a cikin garin Katsina, inda taron ya samu Bakuncin Mambobin ƙungiyar daga Shiyoyin Daura da Funtua, da manyan baki daga Cikin garin na Katsina, acikin bakin da suka samu halartar taron akwai Ɗanmajalisa me wakiltar Karamar Hukumar katsina, Alhaji Abubakar Ali Al’baba. da sauran baki .

dayake jawabi a wajen taron Shugaban kungiyar Comrade Lawal Rabe Lemoo ya bada tarihin kafuwar kungiyar a takaice sana kuma ya kara tuni game da irin aikace-aikacen kungiyar da manufofinta, gami da abinda ya rataya akan Membobinta.

da yake tofa Al’barkacin bakinsa Ɗanmajalisa Hon. Ali Abubakar Al’baba yayi kira ga kungiyar da su kara tsarkake kungiyar tasu, duba da yanda kungiyar take samar da aiyukanyi ga Matasa.

bayan nishaɗantar da baki Hajiya Jummai daya daga Cikin bakin kuma mai fafutaka akan tarbiyya ga matasa da faɗakarwa akan Illar fyaɗe tayi ta’aliƙi me mahimmanci akan halin da ake ciki na lalacewar zamani da gurbacewar tarbiyya, inda tayi kira da kuma neman haɗin kan kungiyar ta MOPPAN da samar da wani yanayi da zai sanya su dunga faɗakarwa game da halin fyaɗe da ake fama dashi a wannan zamani.

Taron ya gudana a Muhallin ƙungiya’yan jaridu ta ƙasa reshen jihar ta katsina dake Unguwar Láyout a cikin garin Katsina da Misalin karfe shadaya na safe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

Shugaba Buhari ya nemi kasashen duniya su yafewa Najeriya bashin da suke binta

A yayin da yake gabatar da jawabi a zauren majalisar dinkin duniya a ranar Juma'a. Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nemi manyan kasashen duniya...

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina

Bangaren aikin jarida na H.U.K Poly sun yaye kwararrin ‘yan social media a Katsina Saifullahi Kuraye‎ September 24, 2021 2 min read Bangaren aikin jarida na...

Hukumar Hana Fasa ƙwabri ta ƙasa wato Custom ta ƙwato Babura Ɗari Biyu da Biyu a Jihar Katsina…

Shugaban Hukumar Ƙwastam na Jihar Katsina Mr. Chedi ne ya bayyana hakan ne a Yau Juma'a cewa tsakanin watan Agusta zuwa Satumba Hukumar ta...

Dan Najeriya ya fiye tsogwami: da ₦500 kacal sai aci a ƙoshi……Inji farfesa Segun Ajibola

Da Naira Dari Biyar ( 500 ) kacal Zaka Iyaci Ka Koshi a Najeriya, Cewar Wani Farfesa, Masanin Tattalin arziki... Tsohon shugaban kwalejin ma'aikatan bankin...

Rail project will not displace host communities-FG

Radio Nigeria The Federal Ministry of Transport and that of Environment have given assurance to residents along the proposed stretch of land demarcated for the...
%d bloggers like this: