TARON GAUGAWA AKAN TSARO SHINE YA RUSHE HALARTAN TARON MAJALISAR YANKIN KUDU MASO KUDU, INJI FADAR SHUGABAN KASA.
Daga: Abdulhakim Muktar
Fadar Shugaban kasa tana farin cikin bayanin cewa, Rashin halartan wakilan Gwamnatin Tarayya a taron da aka shirya na Gwamnoni da masu ruwa da tsaki na yankin Kudu maso Kudu, yasamu wajabci ne sakamakon taron Gaugawa kan tsaro da shugaban kasa ya kira, tabbas ba ko don rashin Girmamawa bane.
Wakilan Taron, karkashin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban kasa Farfesa Ibrahim Gambari, Ministochi da Shugaban nin Tsaro dana hukumar tattara bayanan Sirri sun kammala Shiryawa kan aniyar su na zuwa Port Harcourt domin halartan taron kafin abasu umarnin su dawo saboda Taron Gaugawa kan tsaro.
Wannan Sanarwa da uzurin daya janyo haka tuni aka shaida wa Wa’anda suka Shirya taron ta hanyoyin da mukeda yakinin shine mafi Dacewa.
Kamar yadda ke kunshe cikin Sanarwa da Ministan Harkokkin ‘yan sanda Muhammad Maigari Dingyadi ya kunsa, taron Majalisar Tsaro ta kasa wanda ba Safai yakan zo ba, karkashin Jagorancin Shugaban kasa, an kira taron ne sakamakon hangen yanayin tsaro daya shafi dukkan sassan kasar nan, ciki harda yankin Kudu maso Kudu biyo bayan zanga zangar #Endsars, dakuma bukatar a tsayawa don kare tsaron kasa da Mutuncinta.
Shugaban kasa ya tsaya kyam da himmatuwa don ji bayani daga Shugabanni, Masu ruwa da tsaki da Matasan mu kan abubuwa dake wanzuwa daya shafi dukkkan Sassan Tarayya, a sakamakon wannan, Za’a sake cimma yarjejeniyar sanya wata rana don ganawa da shugaban nin da mahukunta a yankin Kudu maso Kudu bayan an tattauna da juna.
Har wa yau, anyi nadamar dalilin da baza’ iya kauce masa ba, daya janyo fasa taron.