Advert
Home Sashen Hausa Taron Dallazawa a Katsina; Malam Ummarun Dallaje, Sarkin Katsina na Farko daga...

Taron Dallazawa a Katsina; Malam Ummarun Dallaje, Sarkin Katsina na Farko daga Zuriyar Fulani, Shine ya Kafa Daular Musulunci a Katsina,

Taron Dallazawa a Katsina; Malam Ummarun Dallaje, Sarkin Katsina na Farko daga Zuriyar Fulani, Shine ya Kafa Daular Musulunci a Katsina,

Zaharaddeen Ishaq Abubakar @ Katsina City News

Kamar bara, bana ma, Ƙungiyar nan ta Zuriyar Dallazawa (Malam Ummarun Dallaje Sarkin katsina) sun gudanar da Babban Taro karo na biyu a katsina,

Taron wanda aka gabatar a Babban Dakin taro na Jami’ar Ummaru Musa, yasamu halartar Baki, kuma zuriyar Dallazawa daga Bauchi, Adamawa, Gombe Naija, da wasu sassa na  Jihar Katsina, inda aka gabatar da Ƙasidu daban-daban.

Da yake gabatar da jawabi a Madadin Mai martaba Sarkin Katsina, Farfesa Sani Abubakr Lugga, ya ja Hankali, gami da karfafa Zuriyar, da cewa:  “Lallai su mahimmantar da Rubutu, inda ya bada tarihin Shehin Malami Al’maghili, da Makarantar Gobarau, wanda yace Gobarau wata jami’ace Babba ta Ilimi da Rubutu. Ya kara da cewa akwai Manyan Malamai da sukayi Jihadi Irin na Shehu Danfodiyo amma rashin Rubutu yasa ba’asansu ba.

Yace,Rubutu shine Ilimin da zai iya amfanuwa ko bayan ba rai, Idan da ba’a rubutu ba zamu san wanene Ummarun Dallaje ba” Inda ya maimaita Kalmar ayi rubutu har sau uku.

Shima Farfesa Sambo wali Janaidu, (Wazirin Sokoto) Wakilin Mai Martaba Sarkin Musulmi, a madadin Sarkin Musulmi ya yi nasiha da jan Hankali, gami da Nuna alaƙa ta ƙud da ƙud, dake akwai tsakanin Malam Ummarun Dallaje, da Masarautar Sokoto, dama shi kansa, Wazirin na Sokoto, inda ya bayyana cewa Kabarin Kakansa, yana nan Katsina kusa da Ƙabarin Ummarun Dallaje.

Shugaba Kuma jigon Taron Dakta Sani Abdu Fari, ya bada Tarihin Asalin kafuwar Ƙungiyar, da Dalilin kafata,

Angabar da Ƙasidu, daban-daban daga malamai daban-daban, Irinsu Dakta Uwais, Dakta Abdulsalam, Malam Zaharaddeen Ibrahim Katsina, da Sauransu,

Taron na bana da akaima taken, “Commemoration of the Commencement of the Sokoto Jihad  in Katsina (Jimada Ula) 1228, June 1806) By the Flag bearer Malam Ummarun Dallaje”

Wato Tunawa da Fara Jihadin Sokoto a Katsina (Jimada Ula 1228 June 1806)

Tare da Madaukin Tutar Jihadin Malam Ummarun Dallaje ya samu halartar Wakilin Sarkin Katsina, Wakilin Sarkin Musulmi, Tsohon Girandi kadi, Ahamad Muhammad Batagarawa, Alƙalin Lardi, Alhaji, Ummaru Lafiya Uwar Jiki, Dakta Sani Abdu Fari, Alhaji Murtala Ibrahim Safana, Farfesa Sani Lugga, da sauran su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

ADMISSION FORM IS AVAILABLE @ SILICON HEIGHT INTERNATIONAL COLLEGE KATSINA.

SILICON HEIGHT INTERNATIONAL, SCHOOL WISHES TO INFORM THE GENERAL PUBLIC THAT,THE SALE OF FORMS INTO NURSERY, PRIMARY AND SECONDARY IS STILL ONGOING. THE SCHOOL...

Gwamna Aminu Bello Masari ya buɗe taron shuwagabannin Majalisun jihohin Najeriya a Katsina…

Mai girma Gwamnan Jihar Katsina ya bude taron shugabannin majalisun Dokokin Jihohin Najeriya (36) a kwata na uku, da Jihar ta dauki bakunci. Taron da...

Jihar Katsina ta amshi bakuncin Kakakin majalisun Dokokin Jihohin kasar (36).

A cikin shirye, shiryen gudanar da Babban taron Kungiyar wanda ta sabayi lokaci bayan lokaci, domin tattauna al'amurran da suka shafi kasa. Taken taron na...
%d bloggers like this: