Advert
Home Tarihin Unguwannin Katsina da Kewaye TARIHIN SARAUTAR TURAKI A KATSINA

TARIHIN SARAUTAR TURAKI A KATSINA

TARIHIN SARAUTAR TURAKI A KATSINA.

Sarautar Turaki a Katsina ta Samo aslintane a lokacin mulkin Dallazawa, a wajen shekarar 1835. Kuma zuruar Badawan Katsina sune suka fara wannan Sarautar.

SUWANE NE BADAWA A KATSINA?

Badawan Katsina zuruace wadda suka zo Katsina a lokacin Jihadin Shehu Usman Danfodio a wajen shekarar 1821. Badawan Katsina sun baro Kasar Bade, watau Gashua wadda ke cikin Jihar Yobe ta yanzu da niyyar su amso tutar Jihadi wurin Sarkin Musulmi Muhammadu Bello dake Sokoto. Da suka Isa Sokoto sai Sarkin Musulmi yace masu an gama Jihadi a wajajen su, amma zai basu takarda zuwa Katsina wurin Sarkin Katsina Malam Ummarun Dallaje, suje su taimakama shi yaki da Sarakunan Habe, wadanda suka Koma Maradi da Zama. Wannan shine dalilin zuwan Badawa Katsina.

Da suka iso Katsina sun fara Zama a wurin da yanzu ake ce mashi Rimin Badawa kusa da filin Samji. Anan suka yada zango a karkashin Jagorancin shugaban su Mai suna Muhammadu Dogo.

Jagoran Badawa Muhammadu Dogo Yana da yaya biyu manya daga cikin su akwai 1. Muhammadu Dawai Wanda shi babban su, sai Kuma Muhammadu Agawa.

Shi Muhammadu Dogo ya rasu a Unguwar Rimin Badawa a shekarar 1833, Kuma shine mutum na farko da aka fara rufewa a Makabartar Rimin Badawa dake filin Samji Katsina.

A lokacin mulkin Sarkin Katsina Sadiqu Dan Ummarun Dallaje (1835-1844) ne aka fara nada Turaki Muhammadu Dawai Turakin Katsina. Turaki Dawai Yana daga cikin zuruar Badawan Katsina. Turaki Dawai yayi mulki daga shekarar 1835 zuwa 1861. Tunau Dawai shine babban Dan Turaki Muhammadu Dawai. Daga cikin sauran zuri’ar Turaki Dawai akwai 1. Late Alhaji Abdu Baraya Katsina 2. Late Kofur Bello. 3. Jibril Akwance. 4. Alhaji Aminu Abdullahi Barayan Katsina (Deputy Commandent Generel NSCD retired). 6. Barrister Ahmed Abdu Barayan Bade. Da sauransu.

Turaki na biyu daga cikin Zuruar Badawan Katsina shine.

TURAKI AGAWA (1861-1903). Turaki Agawa kanen Turaki Dawai ne. Yayi Turakin Katsina daga shekarar 1861 zuwa 1903. Turaki Agawa ya rasu a shekarar 1903. Kabarin Turaki Agawa ya nan Yana kallon gidan Sarkin Katsina an rubuta Turaki Agawa. Daga cikin Zuruar Turaki Agawa akwai. 1. Late Alhaji Mamnan Dawai Katsina (retire Perm. Sec. KADUNA State Ministry for Local government and Chieftancy Affairs). 2. Late Alhaji Abu Yaro ( First Accountant General Katsina State ). 3. Dr. Mustapha Abu Yaro(Director National Eye Centre KADUNA). 4. Alhaji Aminu Tukur Kofar Bai( High Court Judge Katsina State. 5. Engineer Iro Gambo ( Director Voter Registry Department INEC National Headqueyers Abuja). 6. Alhaji Abu Lili Director D S S). 7. Alhaji Abu Bazariye (Former Chairman Teachers Registration Council of Nigeria). 8. Alhaji Ibrahim Sayyadi former Secretary to the Katsina State government. Da sauran su.

Turaki na Ukku daga cikin Zuruar Badawan Katsina shine Turaki Muhammadu Ladan. An nada Turaki Muhammadu a shekarar 1904 a lokacin mulkin Sarkin Katsina Abubakar. Abubakar yayi Sarkin Katsina daga shekarar (1887-1905). Turaki Muhammadu ya rasu a Makka a shekarar 1922 a lokacin da suka je Aikin Hajii da Sarki Dikko.

Turaki na hudu daga cikin Zuruar Badawan Katsina shine.

Turaki Jari. Turaki Jari ya rasu a shekarar 1933. Sai Kuma Turaki na biyar daga cikin Zuruar Badawan Katsina shine Turaki Sule Bawa. Kuma shine Turaki na karshe daga cikin Zuruar Badawan Katsina. Turaki Sule Bawa ya rasu a Ranar 11-4-1963. Daga wannan lokacin ne Sarautar Turakin Katsina ta tashi daga gidan Badawan Katsina ta Koma gidan Tarno.

Alokacin mulkin Sarkin Katsina Alhaji Sir Usman Nagogo ne Sarautar Turakin Katsina ta Koma gidan Tarno.

Alokacin aka nada Alhaji Isiyaku a matsayin Turakin Katsina, Alhaji Isiyaku shine babban Dan Tarno Barka. Bayan rasuwar Alhaji Isiyaku sai aka nada Alhaji Sani Store a matsayin Turakin Katsina. Daga Alhaji Kuma, sai aka nada dansa watau Dr. Sule Sani Store a matsayin Turakin Katsina. A takaice wannan shine asalin Tarihin Sarautar Turakin Katsina, wadda aka farayin ta a lokacin Mulkin Dallazawa.

Alhaji Musa Gambo Kofar Soro.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

ADMISSION FORM IS AVAILABLE @ SILICON HEIGHT INTERNATIONAL COLLEGE KATSINA.

SILICON HEIGHT INTERNATIONAL, SCHOOL WISHES TO INFORM THE GENERAL PUBLIC THAT,THE SALE OF FORMS INTO NURSERY, PRIMARY AND SECONDARY IS STILL ONGOING. THE SCHOOL...

Gwamna Aminu Bello Masari ya buɗe taron shuwagabannin Majalisun jihohin Najeriya a Katsina…

Mai girma Gwamnan Jihar Katsina ya bude taron shugabannin majalisun Dokokin Jihohin Najeriya (36) a kwata na uku, da Jihar ta dauki bakunci. Taron da...

Jihar Katsina ta amshi bakuncin Kakakin majalisun Dokokin Jihohin kasar (36).

A cikin shirye, shiryen gudanar da Babban taron Kungiyar wanda ta sabayi lokaci bayan lokaci, domin tattauna al'amurran da suka shafi kasa. Taken taron na...
%d bloggers like this: