Tarihin Sabon Shugaban Sojojin Najeriya Manjo Janar Ibrahim Attahiru…

Daga Abubakar A Adam Babankyauta.

Da farko dai Yakamata mai karatu yasan waye sabon Shugaban Sojojin Najeriya Manjo Janar Ibrahim Attahiru.

Manjo Janar Ibrahim Attahiru shi ne ya maye gurbin Janar Tukur Yusuf Buratai babban hafsan sojan ƙasa.

An haifi Manjo Janar Ibrahim Attahiru a ranar goma ga Watan Ogusta na shekarar 1966.

Manjo Janar Ibrahim Attahiru ya shiga aikin soja a cikin kwas na rundunar ta 35 wato Regular Course 35 of Nigerian Defence Academy da turanci.

Janar Attahiru ɗan asalin jihar Kaduna ne a arewacin Najeriya.

Kafin ba shi wannan muƙamin, Manjo Janar Attahiru shi ne shugaban runduna ta 82 a rundunar sojin Najeriya.

Ya taba jagorantar yaƙi da ƙungiyar Boko Haram amma a shekarar 2017 ne Janar Tukur Buratai ya sauke shi daga muƙamin bayan wasu hare-hare da ‘yan bindiga suka kai inda aka kashe wasu mutane 50 a lokacin da suke sallah a masallaci.

A ranar 26 ga watan Junairu, 2021, aka bada sanarwar cewa Manjo-Janar Ibrahim Attahiru, ya zama sabon shugaban hafsun sojojin kasan Najeriya.

Kusan shekaru uku da su ka wuce kenan da shugaban hafsun sojojin kasa mai barin-gado, Lafatana-Janar Tukur Yusuf Buratai ya tsige Janar Ibrahim Attahiru.

Shugaban sojojin kasa mai barin gado Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya sauke Manjo Janar Ibrahim Attahiru ne a sakamakon yin kasa a gwiwa a yakin da ake yi da ‘yan ta’addan kungiyar Boko Haram.

Majiyar mu ta tabbatar mana da cewa a watan Yulin 2017, Tukur Buratai ya ba Attahiru Ibrahim wa’adin kwanaki 40 ya kawo masa kan shugaban yan Ta,addan Boko haram Abubakar Shekau.

Janar Ibrahim Attahiru bai yi nasarar hakan ba, har gobe kuma shugaban ‘yan ta’addan bai shiga hannu ba.

A karshe sai aka ga hare-haren mayakan yan ta’addan ya karu, inda aka rika kai wa jami’an tsaro farmaki har gidan soja, a wannan lokaci ne kuma harin bakin wake ya yawaita.

Asali ma abin da ya faru shi ne, bayan wata daya da nada Ibrahim a matsayin shugaban sojojin da ke yaki da Boko Haram, ‘yan ta’addan suka kai hari har Maiduguri.

A wannan lokaci ne kuma sojojin kungiyar Boko Haram suka kai wa wasu masana daga jami’ar Maiduguri farmakin da su ka yi nasarar kashe wasu sojojin kasa 12.

‘Yan ta’addan sun kuma yi nasarar hallaka wasu ma’aikatan NNPC a wannan harin da su ka kai.

Daga baya an kai hari a wani masallaci inda aka kashe mutane 50.

Watanni shida da nada wannan jami’i, Janar Tukur Buratai ya fahimci gazawarsa, ya fatattake shi daga ofis, ya nada Manjo-Janar Rogers Nicholas a madadinsa.

A ranar 6 ga watan Disamban 2017, babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya tsige babban kwamandan Sojoji a filin daga dake jihar Borno.

A wata sanarwa da ta fito daga Janar Sani Usman Kukasheka, Manjo Janar Nicholas ne ya maye gurbin Manjo Janar Ibrahim Attahiru a matsayin jagoran Operation Lafiya Dole.

A wannan lokaci mayakan kungiyar Boko Haram sun yi ta kai munanan hare-hare a yankin arewa maso gabas, musamman a jihohin Adamawa, Yobe, da Borno.

Mun kawo maku wannan tarihin ne badan Komi ba sai dan kusan waye sabon Shugaban Sojojin Najeriya.

Amma muna Rokon Ubangiji Allah ya bama manjo Janar Ibrahim Attahiru da sauran manyan Hafsoshin Najeriya ikon Sauke Nauyin Dake Kan Su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here