Advert
Home Tarihin Kasar Katsina TARIHIN KOFOFIN GARIN KATSINA

TARIHIN KOFOFIN GARIN KATSINA

*TARIHIN KOFOFIN GARIN KATSINA*

(Kofar Sauri Da Makwabtanta)

Kofar Sauri, kofa ce da ke gabas maso arewa da birnin Katsina. A yamma da kofar, ta yi iyaka da Unguwar Rafukka,Nasarawa, Makera da Yammawa.
Za mu yi bayanin kofar Sauri din, da kuma unguwannin da ke kusa da ita. Akwai bayanai guda biyu game da asalin wannan kofa ta
sauri, a wani bayanin, an ce, kofar Sauri, ta samo asalin ne daga Shugaban samari, wanda ake kira da Sarkin samari, sannan ya zauna a daidai kofar ta Sauri. Yau da gobe ta sanya aka fara takaita kalmar ‘Samari’ zuwa ‘Samri’, daga
nan kuma ta koma ‘Sauri’ inda a karshe kuma ta koma kofar Sauri.

A wani bayanin kuma an nuna cewa, a lokacin mulkin Ummarun Dallaje ne (1807-1835) wani mayaki da ake kira Danbaskore ya kawo wa Katsina hari ta wannan bangare, amma sai ya iske duk kofofin garin a kulle. Sai Sarkin Sauri,
wanda wani gari ne da ke can wajen Kaita ta yanzu, ya kawo wa Katsina gudunmawa ya fatattaki Danbaskore da mayakansa. Bayan ya kori maharan, sai Sauri ya sa aka fasa
kofa ta cikin ganuwar, ya kutsa kai, ya shiga birnin, ya shaida wa Sarkin Katsina duk abin da ya faru. Jin dadin wanan aiki
da Sauri ya yi, ya sa aka sanya wa wannan kofa sunansa,

ma’ana kofar Sauri.
A nan za a iya cewa , ita wanan kofa bata kai sauran kofofin
Katsina tsufa ba, domin kuwa an yi ta ne a Shekara ta 1807.
Amma wasu masana Tarihi suna ganin cewa, akwai kofar
tuntuni, kuma an gina ta ne a karni na 15 a daidai lokacin da
aka gina sauran kofofin ganuwar ta Katsina. Kuma ta
wannan kofa ce fataken da suka tawo daga Kasashen
Larabawa da Agadas da Damagaran da Kaita da Shinkafi
suke bi su shiga birnin Katsina. Haka nan sauran unguwanin
da ke Yammawa da Makera da Nasarawa, dadaddun wurare
ne wadanda tun lokacin kafuwar Katsina suna nan a inda
suke a halin yanzu.

Bayani ya nuna cewa, saboda dinbin dukiyar da ke shigowa
ta wannan kofa ne ‘yan fashi suka rika matsa wa fataken da
ke shiga ta kofar. Ba a samu saukin haka ba sai da Sarkin
Katsina na wancan lokacin ya hada kungiyar ‘yan sintiri na
mayaka, wadanda suka rika gadin kofar.
Kofar Sauri ta kunshi jinsin mutane iri-iri. Akwai adi Habe,
wadanda su ne ainihin mutanen farko da suke zaune a kusa
da kofar Sauri, tun kafin wata al’umma ta zo wurin tare da
Haben da suka iske. Su wadannan Buzaye, asalinsu daga
Agadas ne, wadanda suka rika zuwa Katsina fatauci. Sun
kasance, suna kawo kanwa da dabino da gishiri da kantu da
sauransu, wasu kuma, suna kira. Wadannan mutanen ne ma
tushen kafuwar unguwar Makera da ke Nasarawa Rafukka. In
sun zo, suna yada zango a gidan Sarkin Zango da ke nan
kofar Sauri. A hanjali suka gina rijiya da gidajen zama.

(Kofar Guga Da Makwabtanta)
Kofar Guga, kofa ce da ke yamma maso arewacin birnin
Katsina. Daga cikin kofar, ta yi makwabtaka da unguwar
Sararin tsako da Sullubawa. A wajenta kuwa, ta yi
makwabtaka da Tudun ‘Yan Lifidda da Masallacin Idi na
Katsina.

Za mu yi bayanin kofar Guga da kuma
unguwannnin da ke makwabtaka da ita.
Kofar Guga na da sunaye iri uku: kofar Yamma, wadda aka
sanya mata saboda kasancewar ta a Yammacin birni . Akwai
sunan kofar Tsaro , saboda a da a nan ake ajiye mayaka
masu tsaron kofar, koda za a kawo wa garin hari, amma
sunan dai da aka fi sanin kofar da shi shi ne, kofar Guga . Ita
wanan kalma ta Guga sunan matar Sarkin Gobir ce , Bawa
Jan Gwarzo, wadda aka ce ta gudo ta zo Katsina , ta kuma
shiga birnin na Katsina ta wanan kofar,domin ta fallasa
shirye-shiryen maigidanta ga Sarkin Katsina Muhammadu
Jan Hazo (1740-1751).

Wanan fallasa asiri da Guga ta yi, ya taimaka wajen cin
Gobirawa da yaki a kwafsawar da aka yi bayan zuwan nata .
Don jin dadin wannan nasara ne, Sarkin Katsina Jan Hazo,
ya sanya wa wannan kofa sunan matar, wato Guga. Kofar
Guga na daya daga cikn kofofin da aka fara ginawa a farko-
farkon karni na 15. Kofar ce ake bi a je Gobir wadda a yanzu
ke kasar Sakkwato . Har ila yau , ta kofar ce ake bi zuwa
Bugaje da Jibiya da Maradi.

(Kofar Durbi Da Makwabtanta)
An sanya wa wannan kofa sunan Durbi ne saboda wani
Hakimi na Habe, mai suna Durbi, wanda shi ne Hakimin
kasar Mani tun a wajen karni na 15. Ta wannan kofar ce
yake fita zuwa Mani, ta nan ne kuma yake shiga idan ya
dawo. Daga shi wannan Hakimi na Mani ne aka rika kiran shi
da Durbi.
A wani bayanin kuma, an nuna cewa, wannan kofa mai suna
Kofar Durbi, ta samo sunanta daga sarautar Durbi-Ta-
kusheyi. To daga nan ne, sunan Durbi ya fara a mulkin
Katsina gaba daya, wanda kuma, ko da su Durbawar suka yi
kaura, suka koma birnin Katsina, aka bar sarautar Durbi din
da sunanta na asali, wato, maimakon Durbi sai ta zama
Durbi Katsina.
A yanzu duk wanda ke rike da sarautar Durbi,
shi ne kuma Hakimin Mani. Tun daga Durbi Saddiku wanda
aka yi a shekara ta 1810-1835, an kuma yi Durbi Fandiku
(1836-1860) Durbi Gidado (1860-1883), Durbi Dikko
(1891-1906), har dai ya zuwa yanzu din nan. Ta ita wannan
kofar yake shiga in ya dawo kofar Durbi ta yi makwabtaka
da unguwannin da ke cikin ta, kamar unguwar Filin Samji da
Rimin Badawa. Daga wajen ta kuwa akwai kuma unguwar
Turaka, wato Bariki ko G.R.a.

(Kofar Kaura Da Makwabtanta)
Wannan kofa ta Kaura, ta samu asali ne daga wani mutum
da ake kira Kaura Gumari, wanda Habe ne, kuma mayaki. Ya
zauna tare da iyalansa a Garama da ke nan kusa da kofar.
Kamar yadda majiyarmu ta nuna, bayani ya nuna cewa, wasu
daga cikin ‘yan’uwan wannan mutun sun yi kaura zuwa
Tasawa wanda yanzu ke Kasar Nijar, wasu kuma suka yi
kaura zuwa tsafe a inda suka kafa mulkinsu a can wuraren.
An ce, Zuriyar wannan mutun ne ke mulkin Tasawa da Tsafe.

Amma , a wani bayanin an nuna cewa, kofar Kaura, ta sami
sunanta ne a dalilin Kaura Abubakar, wanda ya yi yake-yake
a lokacin mulkin Dallazawa saboda kwazon wannan jarumi
ne aka ba shi mulkin kula da garin Rimi da ke gabacin
Katsina. Ta wannan kofar ce, shi Kaura Abubakar ke bi ya
fita zuwa Rimi ta nan ne kuma yake dawowa. Karewa da
kaura, a nan kusa da kofar ce ya gina gidansa na kaura,
wanda gidan har yanzu yana nan a matsayin gidan saukar
duk kauran Katsina, Hakimin Rimi.

Kofar Kaura, tana daya daga cikin kofofin birnin Katsina da
aka gina a karni na 15. A wajen kofar Kaura an sami kafuwar
wani gari da ake kira Dandagoro wanda nisan shi da kofar
bai wuce kilomita 3 zuwa 4 ba. A cikin kofar kuwa, akwai
unguwar Shararar Fayif.

(Kofar Kwaya Da Makwabtanta)
Wannan kofa ta kwaya ta samo asali ne daga wani
Basaraken Habe mai suna Sarkin kwaya, wanda ke mulki a
wani gari da ake kira kwaya, da ke kudu da birnin Katsina.
Aikin wannan Basarake shi ne, sama wa Sarki hatsi, kamar
su dawa da gero da sauransu, domin amfanin gidan Sarkin.
An ce, ta ita wannan kofar ce Wali Jodoma, wanda Sarkin
Katsina na lokacin ya kora, ya bi ya fita ya bar Katsina.
Labarin ya nuna cewa, da shi wannan Waliyyin ya fita, sai ya
juya baya ya tsine wa kofar ya ce, “ba za a yi wani abin kirki
a kofar ba, sai bayan shekara dari biyar.” Ga yadda
Katsinawa ke cewa, kusan kowace kofa ta sami ci gaba,
gidaje sun isa kusa da su in ban kofar kwaya. To, amma
yanzu din nan, da take ci gaba, shekaru dari biyar din ne
suka cika. Ita ma wannan kofar, ana jin cewa a karni na 15
ne aka gina ta.

Ita ce ake fita a je garuruwan Dutsinmma da
Safana da Runka har zuwa Kankara.
Alal hakika, kofar Kwaya, a halin yanzu, ta wuce sauran
kofofin ci gaba. Ta kofar ce, ake bi a je manyan-manyan
Makarantun Boko na Katsina. Misali, a kudu da kofar Kwaya
aka gina ‘Federal College of Education’, da Hassan Usman
Katsina Polytechnic ‘ da Katsina Unibersity’ da Umaru Musa
‘Yar’adua Unibersity’ daga shekarar 1980 zuwa yanzu. Baya
ga wadancan, ga babbar kasuwar Katsina ‘Katsina Central
Market’ da babbar tashar, mai daukar fasinjoji zuwa
kudancin Katsina zuwa Funtua, Kaduna, Lagos da sauransu,
wadanda aka yi wajen shekarar 1989. Ga kuma sabon
asibitin kashi da aka gina.

Kofar Kwaya ta yi makwabtaka da wasu unguwanni a cikinta
da wajenta. A cikin kofar Kwaya akwai shararar Fayif wadda
ta kafu ba-baya nan, da bai wuce shekaru 60 ba. A kusa da
kofar daga ciki, akwai shaharariyar Kwalejin nan ta Arabiya
wato ‘Arabic Teachers College’, wadda aka gina a shekara
ta 1967 da kuma gidan hamshakin dan kasuwa, mashahuri,
mai suna Dahiru Barau Mangal. A wajen kofar kwaya, akwai
wata unguwa, wadda ita ma, ba ta wuce shekaru 60 da
kafuwa ba. Wannan unguwar, ita ce sabuwar unguwa.

(Kofar ‘Yandaka Da Makwabtanta)
Kofar ‘Yandaka tsohuwar kofa ce da aka gina a karni na 15.
Ta samo sunanta ne daga Basaraken Habe na garin
‘Yandaka da ke yammacin birnin Katsina. Ta wannan kofar
ce ‘Yandaka ke bi idan zai fita zuwa ‘Yandaka, ta nan ne
kuma yake shiga in ya dawo Kofar ‘Yandaka ta yi
makwabtaka da Gafai daga arewa; Masanawa daga gabas,
tare da Marinar Kadabo da ‘Yantaba, duk daga gabas din.

A kudu kuwa, za a iya cewa, Kofar ta yi makwabtaka da
rafindadi, mun dai riga mun yi bayanin Rafindadin Gafai da
Masasanawa. Yanzu wadanda suka rage, ba mu ce komai a
kansu ba, su ne Marinar Kadabo da “Yantaba. Dukkan
wadannan unguwanni da muka ambata, suna cikin ganuwar
garin na unguwar kofar “Yandaka. A wajen kofar, akwai wasu
wurare masu muhimmanci da za mu yi magana a kansu,
kamar garin babbar Ruga da Filin Folo na Katsina, wadanda
duk suke a yamma da kofar ‘Yandakan.

(Kofar Marusa Da Makwabtanta)
An gina kofar Marusa a wajen karni na 15. Ana jin an gina ta
ne a daidai lokacin da aka gina sauran ganuwowin Katsina,
kuma ta sami sunanta ne daga wani Basarake na Habe da
ke mulkin Dutsi, mai suna Marusa Usman. Ta wannan kofar
ce Marusa din ke bi in zai tafi Dutsi, ta nan ne kuma yake
shiga idan ya dawo. Daga nan ne aka sanya mata sunan
Basaraken ta zama kofar Marusa Usman.
Kofar Marusa, ta yi makwabtaka da wasu unguwanni da ke
cikin kofar da wadanda ke wajen ta. Akwai dai unguwar
Kerau daga cikin ta wanda shekarunta ba su wuce 60 da
kafuwa ba, koda yake, a da can, tun lokacin mulkin Habe har
ya zuwa na Dallazawa, an yi wani wuri da ake kira unguwar
Dantura, wadda a halin yanzu babu wannan unguwa saboda
Kerau ta hade ta, ta koma cikin Kerau din.

(WACCE KOFA CE BAMU KAWO TARIHINTA BA?)

#BARDE🙏

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE BUHARI ADMINISTRATION SUPPORTS THE LAGOS STATE RAILWAY PROJECT!

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/232549375628254/

Kotu ta rushe shugabacin jam’iyar APC ɓangaren Ministan Ilimi, Adamu Adamu a Bauchi

Babbar kotu a Jihar Bauchi ta rushe shugabacin Babayo Ali Misau na jam'iyar APC a jihar. Rahotanni sun baiyana cewa shi dai Misau yaron Ministan...

2023: Don’t Allow Politicians to Use You, Atiku Group Tells Youths

2023: Don’t Allow Politicians to Use You, Atiku Group Tells Youths editorDecember 5, 2021 4:50 Pm Francis Sardauna in Katsina Ahead of the 2023 general election, the...

‘Yan Bindiga Sun Tsananta Kai Hare-hare Akan Hanyar Gusau Zuwa Shinkafi

Daga Dauda Umar Januhu 'Yan Bindiga a jihar Zamfara suna cigaba da kai zafafan hare-hare tare da sace mutane akan babbar hanyar da ta tashi...

DSS sun kama Janar Dambazau a Kano…

DSS sun kama Janar Dambazau a Kano Jami'an Ƴan sandan Farin Kaya, DSS sun kama Janar Idris Dambazau, Shugaban Hukumar Kare Haƙƙin mai Sayan Kaya...