Ta yaya yazo Katsina…?
Wanene Mamallakin Keken…?
A yakin Duniya na biyu da aka fara a ranar biyu 2 ga watan Satumba 1939, aka gama shi daya 1 ga Watan Satumba 1945.
Akwai wani Soja a ana kiransa da Malam Ibrahim mai Kasuwa Kofar Sauri, yana cikin Sojojin da akaje da su yakin Duniyar.
Ya sayi Keken ne ta hanyar tara Alawuns din da ake bashi, a hankali ya rika tarawa, ya sayi Keken tun daga Jamus (Germany) da aka gama yakin Duniya na biyu, aka dauko mashi Keken zuwa Legas daga nan aka daukoshi zuwa Kano, aka sanyoshi cikin Lodi dashi da Kekenshi aka kawoshi Katsina. Don haka shine Keke na Farko da ya fara zuwa Katsina. Shekarunsa 77.