Hawan Bariki ya samo asalin shi a Katsina a lokacin mulkin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko (1906-1944 ).
Shi Sarkin Katsina Alhaji Muhammadu Dikko shine Sarkin days kirkiri Hawan Bariki a Katsina. Yayi wannan ne yaje Bariki ya gaida Resident na Turawa na Katsina. Anan Hakimnai da Magaddai Zasu hadu kowa ya kawo rahotan abinda ke faruwa a garuruwansu wajen Resident na Katsina. Resident na farko a Katsina Wanda Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ya Fara gadawa a Hawan Bariki shine Mr. H. R. Palmer.
Shi dai Palmer kamar yadda Tarihi ya nuna tun farkon zuwan shi a Katsina , mutum na farko daya shaku dashi, shine Sarkin Katsina Muhammadu Dikko, tun ma Sarki Dikkon Yana Durbin Katsina. Alokacinne Sarkin Katsina Abubuakar(1887-1905) ya hada Durbi Dikko da Turawan Mulkin Mallaka, watau ya zama a matsayin liesen officer Tsakanin Turawan Mulkin Mallaka da Sarkin Katsina. Lokacin da Turawa suka tube Sarki Abubakar daga Sarauta a shekarar 1905, Sai suka nada uncle dinshi watau Sarkin Katsina Malam Yero 1905-1906, shi Kuma Yero shima Turawa sun tube shi daga Sarauta a shekarar 1996, to tun daga wannan lokacinne Turawan Mulkin Mallaka suka nada Sarkin Katsina Muhammadu Dikko a matsayin Sarkin Katsina. Daga wannan shekarar ne ta 1907 Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ya Fara Hawan Bariki da niyyar yakai gaisuwa ga Resident din Katsina Mr. H. R. Palmer.
Wannan al'adar ta Hawan Bariki har yanzu ana gudanar da ita a Katsina, a halin yanzu Sarkin Katsina Yana zuwa Bariki ne ko GRA, a wajen Gwamnan Katsina.
Musa Gambo Kofar-soro