Rundunar ƴansanda a jihar Zamfara ta ce jami’anta sun kama wata mata mai suna Fatima Sani bisa zarginta da hannu wajen safarar makamai ga wani ƙasurgumin ɗan bindiga a jihar.
The Cable ta rawaito cewa, da ya ke magana a wani taron manema labarai a jiya Juma’a, mai magana da yawun rundunar ƴansanda a Zamfara, Muhammed Shehu, ya ce an kama wacce ake zargin ne bayan samun bayanai a kan ta.
“A ranar 13 ga Fabrairu, 2023, jami’an ‘yansanda sun kama wata r da aka ambata a sama dauke da harsasai har guda 325, biyo bayan bayanan sirri da aka samu game da ita a garin Lafia a jihar Nasarawa zuwa ga wani dan bindiga da ya yi kaurin suna a dajin Zamfara. ,” inji shi.
“A yayin da ake yi ma ta tambayoyi, wacce ake zargin ta amsa cewa ta shiga sana’ar ne kuma a baya ta yi safarar bindigu kirar AK-47 guda uku da kuma harsashi 1,000 na AK-47 ga ‘yan bindiga da ke aiki a Zamfara.”