Advert
Home Tarihin Kasar Katsina Tarihin garin Muduru....

Tarihin garin Muduru….

TARIHIN GARIN MUDURU

Garin MUDURU na daya daga cikin DAGATTAN gundumar Masarautar Mani. Kuma tana karkashin Karamar Hukumar Mani. Garin MUDURU yayi iyaka da Kasar Durbi ta Kusheyi daga gabas, sannan yayi iyaka da Kasar Rimin guza daga Yamma, Haka Nan ya sake yin iyaka da Kasar Dubi ta Kusheyi daga kudu, sannan yayi iyaka da Kasar Dagacin Gafiya daga Arewa. A halin yanzu Garin na Nan kilometer 29 tsakaninsa da Birni n Katsina akan hanyarka ta zuwa Daura.

Mutumin daya fara kafa Garin MUDURU ana kiransa da suna Malam Dan-ango. Ance ya fito ne daga wajen Katsina tare da iyalinsa da almajiransa wajen shekara ta 1500. Bayan da ya Koma Garin sai ya zauna tare da Jama’arsa ana ta karatu. A na nan sai Jamaa suka Yi ta zuwa wajen wannan Malami domin neman ilimin addinin Musulunci. Daga hakane sai garin yayi ta cika da Baki, har ya Zama Gari sosai.

BAYAN Garin ya bunkasa sai aka bukaci mutanen Garin da su fitar da mutum daya Wanda zai mulkesu. Mutanen Garin basuyi wata wata ba sai suka zabi Malam Dan-ango , shi Kuma Malam Dan-ango sai yaki yarda aba shi shugabancin. Daga Nan yayi fushi yabar Garin. Sai aka ba wani amininshi Mai suna Danbaskore ya Zama shine Sarkin Muduru na farko.

BAYAN Malam Dan-ango yabar Muduru sai mutane sukayi ta yin Kaura suna binshi daga nan sai Garin ya Zama Babu kowa.

A zamanin Sarkin Katsina Ibrahim Maje ne a shekarar (1599) ya bukaci a sake Gina Garin MUDURU. Sarkin ya aika aka dauko wani Malami Mai suna Malam Muhammadu daga Garin “Gunki’ ta Kasar Tsagem a yau ya dawo Muduru tare da iyalinsa da almajiransa ya zauna.

Malam Muhammadu Tarihi ya nuna cewa mutum ne Mai ilimin asirrai, a sabili da hakane yayima Garin kahi, har takai baa iya cin Muduru da Yaki.

A bangaren wadanda suka yi mulkin Muduru Danbaskore shine mutum na farko daya fara Sarauta, daga Nan zuriarsa suka yi ta mulki, Amma .baa samu shekarun da wadannan Sarakunan Habe sukayi mulki ba.

Daga shekarar 1851 ne Dallazawa suka fara mulkin Muduru. Wanda kuwa aka nada shine Muhammadu Musa, Wanda yayi shekara ashirin da bakwai Yana mulki. Bayan rasuwarsa ne aka nada dansa Mai suna Nakande a matsayin Sarkin Muduru a shekara ta 1878.

Sarkin Muduru Nakande Jarumine na Gaske, domin kuwa yaje yake yake da dama. A zamaninsa ne Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ya zauna Muduru, kafin a nada shi Sarautar Giremawa. Kuma anan ne ya auri Goggo watau Mahaifiyar Durbi Ummaru.

Bayan rasuwar Sarkin Muduru Nakande sai aka nada dansa Abubakar a shekara ta 1921, Wanda Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ya nada shi. Sarkin n Muduru Abubakar yayi shekara ashirin da uku Yana mulki, sai Kuma daga baya aka cire shi. Daga nan sai aka maida Sarautar Dagacin Muduru daga Mani, a inda Durbi Ummaru ya nada dansa Mai suna Isah Birema a shekarar 1944.

Bayan rasuwar ne a shekarar 1988 aka ba danshi wakilci Mai suna Umar Isah, Wanda yayi wata daya Yana Wakilci sai wani mahaukaci yazo har cikin fadarsa ya kasheshi. BAYAN rasuwarsa sai aka nada Abubakar Ibrahim a wannan shekara ta 1988.

Sarkin Muduru Abubakar ya rasu acikin shekara ta 2002, daga nan sai aka nada dansa Lawal Abubakar , Wanda har yanzu shine ke mulkin Garin MUDURU har zuwa yanzu.

Alhaji Musa Gambo Kofar Soro.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE BUHARI ADMINISTRATION SUPPORTS THE LAGOS STATE RAILWAY PROJECT!

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/232549375628254/

Kotu ta rushe shugabacin jam’iyar APC ɓangaren Ministan Ilimi, Adamu Adamu a Bauchi

Babbar kotu a Jihar Bauchi ta rushe shugabacin Babayo Ali Misau na jam'iyar APC a jihar. Rahotanni sun baiyana cewa shi dai Misau yaron Ministan...

2023: Don’t Allow Politicians to Use You, Atiku Group Tells Youths

2023: Don’t Allow Politicians to Use You, Atiku Group Tells Youths editorDecember 5, 2021 4:50 Pm Francis Sardauna in Katsina Ahead of the 2023 general election, the...

‘Yan Bindiga Sun Tsananta Kai Hare-hare Akan Hanyar Gusau Zuwa Shinkafi

Daga Dauda Umar Januhu 'Yan Bindiga a jihar Zamfara suna cigaba da kai zafafan hare-hare tare da sace mutane akan babbar hanyar da ta tashi...

DSS sun kama Janar Dambazau a Kano…

DSS sun kama Janar Dambazau a Kano Jami'an Ƴan sandan Farin Kaya, DSS sun kama Janar Idris Dambazau, Shugaban Hukumar Kare Haƙƙin mai Sayan Kaya...