#GaskiyarLamarinNijeriya @Ko kunsaniNG

Ko kun san cewa, a ranar 8 ga Oktoba, 2021, Gwamnatin Shugaba Buhari ta hannun Hukumar Sadarwa ta Ƙasa (NCC) ta bai wa wasu sababbin kamfanonin sadarwa guda huɗu tallafin Naira Miliyan Huɗu, domin bunƙasa harkokin sana’ar sadarwa a Nijeriya, don amfanin tattalin arzikin ƙasar?

Kamfanonin da suka samu cin wannan moriya su ne Clearflow System Hub, Aelaus Engineering Teams/Hyech Electronics Solutions, Kalibotics da CyberNorth Tech. Sun samu wannan gagarumar nasarar ne bayan da suka lashe gasar NCC ta sha’anin amfani da intanet (LOT) ta 2021, inda aka bai wa kowannensu tsabar kuɗi Naira Miliyan biyar.

Biyu daga cikin kamfanonin, wato Clearflow System Hub da Aelaus Engineering Teams/Hyech Electronics Solutions sun samu nasarar ne sakamakon samar da manhajar yaƙi da garkuwa da mutane da kai hare-hare, yayin da kuma kamfanonin Kalibotics da CyberNorth Tech sakamakon samar da manhajae mutum-mutumi mai taimakawa wajen magance matsalolin shara da muhalli.

Wannan na daga cikin irin hanyoyin da Gwamnatin Shugaba Buhari ke bi, don ƙarfafa wa kamfanoni masu tasowa, saboda haɓaka tattalin arzikin ƙasa!

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here