Tallafi: Bola Ahmad Tinubu Ya Ba Da Tallafin Naira Miliyan (N50m) Ga Wadanda Gobarar Babbar Kasuwar Katsina Ta Shafa.

Babban jigo a jam’iyyar (APC) na kasa kuma tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmad Tinubu, ya sanar da bayar da gudummawar zunzurutun kudade har naira Miliyan (N50m) ga wadanda gobara ta shafa a babbar kasuwar jihar Katsina.

Tinubu, ya bayyana hakan ne a yau Laraba a yayin wata ziyarar jaje da ya kai wa ‘yan kasuwar da kuma gwamnatin jihar Katsina.

A yayin ziyarar tasa, gwamnan jihar, Aminu Bello Masari ne ya tarbe shi da sauran manyan jami’an gwamnatin jihar.

Gobarar babbar kasuwar ta Katsina wadda ta faru a ranar Litinin ta lalatar nan da suka gabata, kayayyaki da kadarorin da darajarsu ta kai ta miliyoyin nairori ne gobarar ta lashe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here