TALLA
Manyan nasarorin Gwamna Masari a mawuyacin hali

Duk da cewa wannan hali da kasa ke ciki ba shi ne mafi dacewa na magori, wasa kanka da kanka ba, duba da irin munin tagwayen kalubale na rashin tsaro da anoobar Korona da suka addabi Arewacin kasar nan, ciki har da jihar Katsina, waiwayen tafiyar gwamnatin Masari tun hawanta kujerar mulki zuwa yanzu, ka iya zama abin da Likita zai iya ba da shawarar a yi. Kai shi ne ma sanadarin da ake bukata don dadada wannan hali da ake ciki, a kauce daga munanan labaran da suka yi wa al’umma bakin fenti saboda wadannan masifu masu kona rai.
Ba wani mabudin wannan bayani da ya wuce irin yabo da jinjina ga Gwamna Aminu Bello Masari da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi sau shurin masaki, saboda gamsuwa da irin ayyukan da Gwamnan ya yi, inda ya ciri tuta wajen ingantattun ayyuka masu yawa a jihar da Shugaban kasa ya fito, Katsina.
Duk da irin tsauri da rashin son wargi na Shugaban kasa, sai da ya ce wa Gwamna Masari: “Mun gode Gwamna Masari saboda kula da jama’ar mazabata,” yayin da yake kaddamar da hanyar Fago zuwa Koza da aka sake mata tsari da gini a ranar Alhamis, 15 ga Agusta, 2019.
Haka kuma a sakonsa na fatan alheri a lokacin murnar cikar Gwamnan shekaru saba’in da haihuwa a ranar 29 ga Mayu, 2020, Shugaba Buhari sai da ya sake kada kuri’ar amincewa ga Gwamnan jihar Katsina, inda ya ce, “Gwamna Masari ya yi aiki tukuru wajen farfadowa da daga matsayin sashen Ilimi a jihar Katsina, tare da mai da hankali kan ilimin yara mata da almajirai, inganta kayayyakin more rayuwa, da harkar lafiya ta hanyar daukakawa da fadada dukkan manyan asibitocin jihar da sauran cibiyoyin lafiya.
“Hangen nesan Gwamna Masari da salon mulkinsa na tafiya da kowa, yalwar gogayyar sa da nema wa jama’arsa duk wani abu mai kyau da kasa baki daya, abin koyi ne matuka.”
Kuma bayan ceto dalibai 344 na Makarantar Sakandaren kimiyya ta Kankara da suka yi mako guda a tsare, Shugaban kasa sai da ya sake yin wani yabon mai yawa kan Gwamna Masari saboda irin kwazon da ya sa cikin lamarin har aka samu sakin daliban daga hannun masu garkuwa da su ba tare da asarar rai ko guda ba, wato ya aza yabo da jinjina a gurbin da ya dace.
Duk da wannan kalubale, wanda ya dada munana saboda ’yan gaza-gani da ba su ganin alheri su fada, Gwamnatin Masari ta iya cimma wadannan gagaruman nasarori:

HARKAR ILIMI
Tun sa’ad da wannan gwamnatin ta kama aiki a ranar 29 ga Mayu, 2015, Gwamna Masari ya gaji jiha ce wacce ita ce ta biyu mafi talauci ta fuskacin tattalin arziki, kuma mafi koma baya a harkar ilimi. Wannan mummunan hali ya sha bamban da abin da ya kamaci ya zama makomar Katsina, ganin cewa a baya can ta zama ita ce kan gaba a fannin ilimi da noma a Arewacin kasar nan. Katsina ce gida ga makarantar gaba da firamare ta farko a Arewa, kuma ita ce kan gaba a noman auduga, gyada da hatsi a kasar nan.
Kasantuwarsa a kullum cikin kyakkyawan fata, ya gamsu cewa sauya makomar jihar zuwa ga makoma mafi kyau abu ne mai yiwuwa, saboda amannar da ya yi cewa, “matsala tana ci gaba da zama a haka ne a zuciyar da ta rasa himma da sikkar cewa za a iya kau da ita.” A gun mai girma Gwamna, hatta rashin isassun kudi ba gamsasshen dalili ne na rashin tabuka ayyukan kwarai ba, saboda ba wai yawan kudin da ke hannu ne abin dubawa ba, amma yadda aka yi amfani da abin da ke hannu ta hanyar da ta dace. Kuma wannan hakikar ce ta zame masa falsafar da ke jan ragamar yadda yake tafiyar da harkokin jihar Katsina tun daga ran 29 ga Mayu, 2015.
Magana ta gaskiya ita ce ba wata al’umma da za ta ci gaba fiye da matakin ilimin jama’arta. Wannan ne ya sa a gun Gwamna Masari, ilimi har kullum shi ne “na farko, na biyu kuma na uku mafi muhimmanci,” a gwamnatinsa. Irin daukin da gwamnatin nan ta kai wa wannan sashi, musamman a matakan makarantun firamare da sakandare wani abu ne da ba a taba yin irin sa ba a jihar. Daukin da gwamnatin nan ta kawo bai tsaya kawai ga gyara gine-gine ba, don kuwa inganci (horarwa da sake horarwa), yawa (daukar Malamai) da kyautatawa (karin girma da biyan albashi da sauran hakkoki kan lokaci) na ma’aikatan da ke fannin koyarwa da wadanda ba sa koyarwa, duk sun samu kulawar da ta dace daga gwamnati.
A yayin da azuzuwan da aka gina su a kan daukar dalibai 50 a mafi yawa suke daukan dalibai 150 a makarantun firamare da sakandare, nan da nan gwamnatin Masari ta fara aikin gyara da gina sabbin azuzuwa a duk fadin jihar. Kujeri 15,000 da ke hade da tebura, an sayo su tare da rarraba su.MAKARANTUN FIRAMARE:
Jimillar sabbin azuzuwa 1,026 ne aka gina, kuma azuzuwa 1,268 aka gyara, abin da ya mai da jimillar azuzuwa 2294 aka mai da su cikin kyakkyawan yanayin amfani da su.
Ofisoshin Malaman firamare kuwa, dari da talatin da biyar (135) ne sabbi aka gina, yayin da aka gyara guda 532. Haka nan kuma sito-sito 135 sabbi aka gina, aka gyara guda 532.
Jimillar bandakuna 930 ne aka gina a dukkan makarantun firamaren da ke fadin jihar.
MAKARANTUN SAKANDARE:
Sabbin makarantun Sakandare guda bakwai ne aka gina a duk fadin jihar a kan kudi Naira biliyan 1.1 (N1.1billion).
Makarantun Sakandare guda ashirin da biyar (25) ne a dukkan mazabun Sanatoci uku na jihar ne aka gyara su kwata-kwata da bunkasa su a kan kudi Naira biliyan 3.2 (N3.2billion).
Makarantun sakandare arba’in da takwas (48) da suke fama da rashin kula ga barnar guguwa, aka gyara su tare da farfado da su a kan kudi Naira biliyan 7 (N7billion).
Daga cikin Kwalejojin kimiyya da koyon sana’o’i sha takwas (18) da ke jihar, sha uku (13) aka yi musu gyara gaba daya, aka daukaka su a kan kudi Naira biliyan 2 (N2billion).
Gwamnati ta kara girma tare da biyan dukkan ‘ariyas’ na Malaman Firamare da Sakandare 1100 da ke jihar, wadanda wasun su ba su taba samun karin girma ba fiye da shekaru goma baya.
Dukkanin makarantun mata na jihar an mai da su na kwana.
Baya ga Malamai 2000 da aka dauka na Firamare da Sakandare, yanzu haka akwai wasu 5000 da ake dauka karkashin shirin ‘State Power Programme’.
ILIMIN YARA MATA:
Wannan ma wani sashe ne da gwamnatin Masari ta ba shi matukar kulawa, tana karfafa iyaye, musamman iyaye mata da su tura ’ya’yansu mata zuwa makarantun firamare maimakon tura su talla.
Wannan sashe ya kirkiro shirye-shirye don amfanar iyaye mata, kuma sakamakon da aka samu shi ne gagarumin raguwar yawan yaran da suka cancanci zuwa makaranta da suke yin talla a kan titi.
MAKARANTUN GABA DA SAKANDARE:
Tun daga shekarar 2015 zuwa yau, an kashe kudi N7.32billion kan biyan kudin gurbin karatu ga dalibai ’yan asalin jihar Katsina gami da samar da kayayyakin more rayuwa da hidindimu a makarantun gaba da sakandare hudu mallakin jihar da suka hada da: Jami’ar Umaru Musa ‘’Yar’adua (UMYU), Kwalejin Kimiyya da fasaha ta Hassan Usman Katsina (HUKP), Kwalejin ilimi na Isa Kaita (IKCOED), Kwalejin Dr. Yusuf Bala Usman (YBUC).
KIWON LAFIYA
Gwamnati ta kaddamar da aikin gyara, wasu ma an kammala da kashi 70% na manyan Asibitocin da ke Katsina, Daura, Funtua, Malumfashi, Musawa, Dutsinma, Mani, Baure da Kankiya. Ana yin haka ne kuma tare da sanya musu kayayyakin aiki na zamani don su tafi kafada da kafada da manyan asibitocin kasar nan mafi kyawu.
Haka kuma cibiyoyin samar da lafiya a sauran Kananan Hukumomin da ke jihar sun samu gyaran da ya dace da su.
Gina Asibitin kwararru na idanu da ke Asibitin kwararru na Janar Amadi Rimi, ana gab da kammalawa.
Ya zuwa yanzu an dauki ma’aikatan lafiya 993 aiki, da suka hada da Likitoci 110 (ciki akwai Likitocin tuntuba guda 15), nas-nas 250 da ungozoma 330 da wasu ma’aikatan lafiyan na daban, akwai kuma wani zubin ma’aikatan lafiya 500 da yanzu haka ake shirin daukar su aiki.
Likitoci 30 ne aka ba su cikakken gurbin karatu don su samu kwarewa a fannoni daban-daban. Kwalejin koyon jinya da ungozoma ta dauki Malaman jinya 13 aiki, masu koyar da aikin likita guda biyar da Laccara guda. An kuma ba da gurbin karatu ga  nas-nas: Guda 18 a karatun babbar Difuloma (Nursing Education), hudu za su yi karatun digiri kan aikin nas (BN.Sc), 11 za su karanta digiri na biyu a kan jinya (MSc) da guda uku da ke yin digiri na uku. Haka kuma akwai karin wasu ma’aikatan kiwon lafiya 200 da aka amince musu su yi karatun dukkan lokaci da wasu kuma na wucin-gadi a gida da waje don inganta iliminsu.
Gwamnatin Masari ba kawai ta gyara da kuma bunkasa Kwalejin koyon aikin jinya na Katsina ba ne, ta kuma samo mata takardun tantancewa, a karon farko da ta samu haka tun lokacin da aka kafa ta a 1956, ta kuma nunka adadin daliban da take iya dauka daga 50 zuwa 120.
Kwalejin koyon aikin ungozoma da ke Malumfashi da Kwalejin kimiyyar kiwon lafiya da ke Daura da Kankiya, dukkan su an gyara su, an kuma bunkasa su.
Watakila wani abu mafi burgewa dangane da irin daukin da wannan gwamnatin ta kawo wa sashen lafiya shi ne shirin mai da babban Asibitin gwamnatin Tarayya na Katsina zuwa Asibitin koyarwa na jihar tare da amincewa da goyon bayan Ma’aikatar kiwon lafiya ta Tarayya. Wannan shirin ya kankama, ta yadda da izinin Allah, zai samu hakkakuwa cikin ’yan shekaru kadan.
Haka nan kuma gwamnatin Masari ta gina Cibiyoyin samun lafiya guda 10 a Dajin Rugu saboda Fulani a Kananan Hukumomi goma (Jibia, Batsari, Dutsinma, Safana, Danmusa, Kankara, Faskari, Danja, Sabuwa da Dandume).
Sannan kuma an gina dakunan ma’ajiyar kankara guda uku a Sandamu, Dandume da Kankiya, kuma aka samar musu da ma’ajiyar kankara guda uku, manyan janaretoci guda biyu, da motoci 7 kirar Hilux don jigilar alluran rigakafi.
An kuma kammala gina babbar cibiyar kula da lafiya a Ketare da ke Karamar Hukumar Kankara, a yayin da kuma wata irin ta a Kafur an gyara ta gaba dayanta.
KORONA (COVID 19)
A yayin da matsalar rashin tsaro take dora katon nauyi a kan kudaden jihar da ba su da yawa, sai kuma ga annobar Korona, wato Covid 19 ta kunno mummunan kanta, ta kara nata nauyin kan dan abin da ya yi saura na kudin jihar. Duk da haka dai gwamnatin jihar ba ta yi kasa a gwiwa ba, ta rika fadi-tashin yin abin da ya dace, kuma za ta ci gaba da yi don shawo kan wannan muguwar annoba ta Covid 19.
Wannan kakkarfan kuduri na shawo kan wannan mugunyar cuta mai saurin bazuwa shi ya kai ga kafa wurin kebe jama’a mai daukar gadaje 260 da kuma wasu dakunan daukar gadaje 20, da kuma masu daukar gadaje 10 a Asibitin kashi na Amadi Rimi, Katsina da babban Asibitin Tarayya da ke Katsina.

FANNIN NOMA
Saboda irin muhimmancin da Gwamna Masari ya bai wa wannan sashe, Mataimakinsa, Alhaji Mannir Yakubu ne aka damka wa Ma’aikatar aikin gona a matsayin Kwamishinan ta, wanda kuma sanannen Jami’in tuntuba, Dk. Abba Abdullahi ne zai rika taimaka masa a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkar noma.
A matsayin Katsina na jihar noma, ana damawa da ita sosai a shirin babban bankin Nijeriya na bunkasa noman shinkafa da auduga, a inda Katsina ce ta farko a noman auduga, kuma ta biyu a bayan jihar Kebbi a noman shinkafa.
Noma a Katsina ya samu wani sabon tagomashi ta hanyar samarwa da rarraba takin zamani isasasshe na dukkan nau’o’in takin don saboda noman damina da na rani, ba tare da irin burgar da ake yi duk shekara na kaddamar da rarrabawar ba.
Wani adadin taraktoci da ya dace, wadanda yanzu ma ana hada su a jihar, an sayo su, kuma ana raba su ga manoma bisa rance mai sauki da gwamnati take yi.
Gwamnatin Masari ta kammala shirye-shirye da wani kamfanin kera taraktoci na Indiya da ake kira Mahindra Machines don harhada taraktoci da sauran kayan injunan noma a masana’antar ayyukan karafa da aka farfado da ita da ke Kankiya.
An kuma kafa Tsangayar noma a Jami’ar Umaru Musa ’Yar’aduwa don kara bunkasa fannin noma a jihar.
Wannan jiha ta kasance mai himma a shirin babban bankin Nijeriya na ba da rance don noman shinkafa, a inda manoman shinkafa na jihar suka samu cin gajiyar rancen Naira miliyan 200. Godiya ga irin goyon baya da karfafa gwiwa na gwamnati, wadanda suka samu wancan rance tuni sun biya bashin gaba dayansa dari bisa dari. Yanzu Katsina ita ce ta biyu bayan jihar Kebbi a samar da shinkafa a karkashin wannan shirin.
SAMAR DA RUWAN SHA
A wani gagarumin aikin da ba a taba yin sa a baya ba, aikin farfadowa da bunkasa madatsun ruwa na Ajiwa Dam (don amfanin birnin Katsina da kewaye), Malumfashi Dam (don amfanin garin Malumfashi da kewaye) da Mairuwa Dam (don amfanin Funtuwa da kewaye), da kuma madatsar ruwa ta Daura, gwamnatin Masari ta fara su, wasu ma har an kammala su.
Haka nan kuma saboda hadin kan da muka samu daga gwamnatin Tarayya, ayyukan da aka watsar a baya na madatsun ruwa na Zobe Dam a Dutsinma, Sabke Dam a Daura da Jibia dam a Jibia, yanzu duk an gama su, in banda wasu ’yan gyare-gyare da za a yi kafin kaddamar da su.
Gwamnatin Masari ta kammala dukkan shirye-shirye don cin gajiyar wadannan madatsun ruwa, wadanda sune mafiya girman matattarar ruwa da mutum ya gina a kasar nan don yin noman rani.
Akwai wasu kananan madatsun ruwa da aka farfado da su, wasu da yawa kuma ana kan gina su a dukkan mazabun Sanatoci uku na jihar don yin noman rani da shayar da dabbobi.
Mafi girman aikin dai shi ne na samar da ruwa na Ajiwa, wanda shi ne babban hanyar samar da ruwan sha ga birnin Katsina, babban birnin jihar da kewaye. Duk wata ma’ajiyar ruwa an rubanya girmanta don tabbatar da samun tsaftataccen ruwan sha a kullum, musamman a manyan cibiyoyi irin su makarantu, da Asibitoci.
BUNKASA MASANA’ANTU
Wani sabon sashe, Hukumar bunkasa zuba jari na jihar Katsina, wato Katsina State Investment Promotion Agency (KIPA), wanda Darakta ke jagoranta, gwamnatin Masari ta bude don bunkasa shirin samar da masana’antu na jihar. Wannan Hukumar tuni ta fara aikinta ka’in da na’in, inda a watanninta na farko ta shirya taron masu zuba jari na kasa da kasa tare da hadin gwiwan manyan kamfanoni na cikin gida irin su rukunin kamfanonin Dangote da BUA, wanda ya samu halartar kamfanonin kas ashen waje daga Chaina, Indiya, UAE, US da UK.
Gwamnatin Gwamna Masari tuni ta gyara wuri, ta kuma haifar da yanayin da ya dace don masu zuba jari su zo su yi harkokinsu na kasuwanci.
Gwamna Masari ya farfado da wasu masana’antu da tuni suka mutu tun lokacin da aka kafa su a 1979 zamanin gwamnatin Gwamna Balarabe Musa na tsohuwar jihar Kaduna a jamhuriya ta biyu. Wadannan sun hada da: Masana’antar karafa da ke Kankiya, masana’antar farar kasa na Kankara, masana’antar yin konannun bulo na Funtuwa da masana’antun jima na Daura da sauransu.
Duk da cewa mutanen Sin sun kafu a jihar Katsina, amma rukunin kamfanonin Dangote ya sami fili don kafa kamfanin noman tumatur da mai da shi na gwangwani.
Rukunin kamfanonin BUA kuma ya nemi gwamnatin jihar don samun filin kafa masana’antar yin zannuwa da dangoginsa.
Wani rukunin masana’antu, wanda babu irin sa a jihohi makwabata, wannan gwamnatin ta riga ta tsara shi don karfafa masu zuba jari da ’yan kasuwa masu zaman kansu su zo su bude harkokinsu na kasuwanci a jihar.
HANYOYI, GIDAJE, DA SUFURI
Sabanin karairayin da makiyan ci gaba ke ta yadawa, gwamnatin Masari ta yi gagarumin hobbasa na kara yawan hanyoyi masu kyau na jihar, duk kuwa da karancin kudin da take fama da shi.
Gwamnatin Masari ta kammala gina dukkan hanyoyin da ta gada daga gwamnatin da ta shude wadanda ba a kammala su ba, wadanda yawancinsu an ba da su ne a gurguje, kuma an dan soma su ne kawai daf da gwamnatin za ta bar mulki a Mayun 2015.
Ya zuwa yanzu gwamnatin Masari ta gina hanyoyi matsu tsawon kilomita 500 wadanda suke kusan daidai a dukkan mazabun Sanatoci uku na jihar. An kuma gina hanyoyin karkara guda 39 da suke da tsawon kilomita 461 a duk fadin Kananan Hukumomin jihar guda 34.
KULA DA AMBALIYAR RUWA
Ambaliyar ruwa a birane da maraya ya riga ya zama ruwan dare, wanda yake aukuwa a duk shekara, ta yadda a kullum magidanta fargabar shigowar damina suke yi. Bisa sanin wannan damuwa da ke damun jama’a a lokacin damina ne, ya sa gwamnatin Masari tun kama aikinta a 2015 ta fuskanci wannan kalubale, a inda ta kashe abin da bai gaza Naira biliyan 2.5 a wani tsari na takaitawa da tsare jihar Katsina daga barnar ambaliyar ruwan sama.
Bisa wani gagarumin shiri, akwai ayyuka da dama a Katsina, babban birnin jihar, Jibia, Malumfashi da Funtuwa, inda aka kashe biliyoyin Naira, wanda ke karkashin shirin gwamnatin jihar da hadin gwiwar bankin duniya mai suna NEWMAP a takaice.
Aikin da ake yi a birnin Katsina da kewaye ya hada da gina wani magudanar ruwa na kankare mai tsawon kilomita 11 da fadin mita biyar, wanda ya taso tun daga Kofar Guga ta Sabuwar Kofa har zuwa gadan Shinkafi.
Wadannan ayyuka wasu sanannun kamfanonin gine-gine ne ke yin su, Mothercat da Triacta, a inda na farkon ke yin ayyuka a Katsina da Jibia, na biyun kuma key i a Malumfashi da Funtuwa.
Ya zuwa yanzu dai gwamnatin Masari ta fara gina gine-ginen kula da ambaliyar ruwa a wurare 122 da suka shafi al’ummu 150 (Wasu ma an kammala su, wasu kuma ana daf da kammalawa).
Wadannan ayyukan sun hada da:
(i)                 Mita 88,537 na magudanar ruwa na kankare
(ii)               Mita 1,910 na wani bangon kare ruwa
(iii)             Mita 360 na wani makarin ruwa
(iv)             Kwalbatoci 104
(v)               Mita 1,550 na wani mazubin ruwa.
A babban birnin jihar da kewaye kawai, wannan dauki da gwamnati ta kawo ya sa an gina magudanar ruwa mai tsawon mita 21,139 na kankare da kuma kwalbatoci 24.
GIDAJE
Wasu rukunin gidaje uku da suka kunshi gidaje 450, yanzu haka ana kan aikin gina su a matakai daban-daban na kammalawa. Gidaje 200 da ke kusa da babban Asibitin Tarayya ma duk an kamala su.
A matsayin Funtuwa na cibiyar harkokin kasuwancin jihar, gwamnatin Masari ta fadada tare da daukaka babbar kasuwar Funtuwa da Tashar motar garin da kashi 50 cikin dari.
Gwamnatin jihar kuma ta fadada Hukumar sufuri ta jihar ta hanyar sabunta motocinta da motoci 30 na samfurin Toyota Costa da bas-bas na Hiace.
TALLAFI
A yayin da Cibiyoyin taimakon jama’a (MDAs) guda bakwai suke cikin shirin ba da tallafi na gwamnati, sama da matasa 15,000 ne suka sami horo da tallafi a kan sana’o’i daban-daban, a inda mata suka fi yawan samun kaso na kashi 60%.
Hukumomin da aka dora wa wannan shiri mai muhimmanci sun hada da Ma’aikatar kimiyya da fasaha, Hukumar KASEED, Ma’aikatar Mata, Sashen kula da ilimin yara mata da Sashen bai wa matasa da mata tallafi.
TSARO
Ganin yadda kimar nagartaccen ilimi da tsaro ba shi da tamka, to babu wani yawan kudi da lokaci da aka kashe a kan wadannan sassan da za a ce ya yi yawa, in aka yi la’akari da illar rashin su a al’umma.
Don kara fahimtar irin nasarorin da gwamnatin Masari ta samu a fannin tsaro, waiwayen halin rashin tsaron da jihar take ciki kafin zuwan gwamnatin APC zai taimaka a kan haka. Matsalar rashin tsaro ta fuskacin satar shanu, garkuwa da jama’a da fyade wadanda suka gurgunta harkokin noma da kasuwanci sosai, wani al’amari ne da ya zama ruwan dare, musamman a Kananan Hukumomi takwas na jihar. Wadannan Kananan Hukumomin suna cikin dajin Rugu, wanda ya zame wani ‘mafakan’ dindindin na wadannan batagari, maharan daji.
Matsalar rashin tsaron nan ta kai intaha ta yadda a wata rana a watan Maris na 2014 yayin da Shugaban kasa na lokacin, Shugaba Goodluck Jonathan da Shugabannin PDP jam’iyya mai mulki na kasa ke gari, wadannan maharan daji suka kashe mutane 142 na wani kauye da ke tsakanin Kananan Hukumomin Faskari da Sabuwa, a wani hari da ya shafe awanni biyar ba tare da an samu taimakon jami’an tsaro ba. Yayin da ya kama aiki, Gwamna Masari sai ya shirya wani aikin hadin gwiwa tsakanin jihohin Katsina, Kano, Kaduna, Jigawa, Zamfara, Sakkwato da Kebbi da kuma jihar Neja da ke tsakiyar Nijeriya.
Sai dai wannan shiri bai dade ba, saboda in banda shi Gwamnan Katsina, duk sauran sun janye, suka gwammace kowa ya yi nasa kokarin a jiharsa. A karshe dai dole Gwamnonin suka sake hadewa don fuskantar matsalar da karfi guda bayan an yi asarar lokaci mai muhimmanci ga wadannan maharan daji.
Ya yi tattaunawar sulhu da tubabbun barayin shanu, wadanda suka mika makamansu a wani shirin gwamnati na yin afuwa a wani biki wanda ya samu halartar manyan jami’an tsaro na soji da ’yan sanda da jami’an tsaron kasa na farin kaya, a inda aka yafe wa tubabbun, kuma da alkawarin inganta rayuwarsu ta hanyar gina musu makarantu, dakunan shan magani da wuraren shayar da dabbobi. Kuma an gina makarantun firamare goma, dakunan shan magani goma da wuraren shan ruwa da dama a wuraren da wannan sulhu ya shafa, kamar yadda Gwamna ya alkawarta.
Ya kuma samar da wani shiri na gano kowace dabbar da ake kiwo bisa hadin gwiwa da kamfanin sadarwa na MTN, wanda zai iya ba da damar gano dabbar da aka sace a Runka da ke Karamar Hukumar Safana ta jihar Katsina a ranar Asabar 2 ga Disamban, 2017.
Babbar bukatar da Gwamna ya nema daga maharin dajin kafin sanya hannu a kan yarjejeniyar sulhun ita ce su watsar da ayyukan daba a ko’ina a fadin kasar nan, ba a Katsina kawai ba.
Wannan yunkuri na samar da zaman lafiya mai dorewa da shugabannin kungiyoyin daban ya gamu da tangarda ne saboda Gwamna Masari ya dage cewa, sai sun aje makamansu, su bar maboyarsu da ke daji, su shigo gari da kauyuka kamar yadda suke a da, a zauna lafiya da sauran jama’a. Wadannan maharansu suka bijire, tare da alkawarin daina ayyukan dabancinsu a jihar Katsina kawai, amma za su ci gaba a sauran jihohi.
Yawan karin sansanonin sojoji da ’yan sanda a jihar Katsina duk ya samu ne a dalilin Gwamna Masari. Kafin shekarar 2016, barikin soja daya ne kawai a jihar, Bataliyar soja ta uku da ke Katsina, amma babu ma wata rundunar sojan sama a lokacin. Amma a yau Katsina tana da Birged na 17 na sojan kasa, bataliya biyu, kowacce a Daura da Malumfashi, da sansanonin sojan sama daya a Katsina, Daura da Funtuwa. Ta bangaren ’yan sanda kuwa, an samu karin wasu rundunonin yanki guda hudu, wanda ya kai adadinsu zuwa shida a yanzu don taimaka wa rundunar ’yan sanda ta jihar Katsina.
Duk da cewa Shugabannin rundunonin tsaro a jihar ba a karkashin Gwamna suke ba, gwamnatin jihar tana daukar nauyin da ya fi karfin aljihunta. Domin kuwa gwamnatin jihar ke biyan alawus na ma’aikatan tsaro a bakin aiki, baya ga taimakon kudi da take bayarwa na wata-wata ga dukkan Hukumomin tsaro da ke jihar. Wannan fa banda taimakon da take bayarwa loto-loto na tafi da ayyuka kamar samar da motocin sufuri irin su Toyota Hillux da mashina.
SATAR ’YAN MAKARANTAR SAKANDAREN KANKARA
Da ba don yabon da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa Gwamna Masari kan kari ba wajen ’yanto daliban makarantar Sakandaren kimiyya na Kankara 344 da aka sace, da tuni wasu ’yan bana-bakwai da ake shakkun gaskiyarsu sun yaudari wadanda ba su da cikakkiyar masaniya wajen ba su nasarar da aka samu a wannan yunkuri na ’yanto yaran nan.
Irin kokarin da Gwamnan ya yi na ’yanto yaran nan, duk da irin sa idon duniya da hakan ya jawo wa jihar Katsina, ya tona asirin karyar da wasu bata gari ke yadawa dangane da wasu manyan gwamnatin jihar Katsina.
HAKKOKIN MA’AIKATA DA WADANDA SUKA YI RITAYA
ALBASHI DA SAURAN HAKKOKI
Wani sashe da har yanzu ba a iya ganin wallen gwamnatin Masari ba shi ne wajen biyan ma’aikata da wadanda suka yi ritaya albashi da sauran hakkokinsu.
Kamar yadda Gwamna Masari ya sha fada ne, albashin ma’aikata da sauran hakkokinsu hakkinsu ne ba tagomashi ba, don haka ba su hakkokin a kan kari wajibi ne ba alfarma ba. Tun da gwamnatin nan ta kama aiki a ranar 29 ga Mayu, 2015, biyan albashi ya dore a kan kari a ranar 25 na kowane wata ko ma kafin hakan.
FENSHO DA GIRATUTI
Tun daga watan Yunin 2015 zuwa Agustan 2020, gwamnatin Masari ta biya jimilla Naira biliyan 71 na fensho da giratuti ga ma’aikatan da suka yi ritaya na jihar da Kananan Hukumomi da Hukumomin ilimi na Kananan Hukumomi.
DAUKAR MA’AIKATA
Daga Junairun 2018 zuwa yau, Hukumomin MDAs, in ka debe na Ma’aikatar ilimi sun dauki ma’aikata 3,080.
KAMMALAWA
Gwamna Aminu Bello Masari ba irin ’yan siyasar nan ba ne masu dadin baki, shi mai fada da cikawa ne. Da ganin Hon. Masari, ka ga dan siyasar da ke aiki da cikawa, mai kaucewa yaudarar siyasa da yin abu don ganin idon jama’a.
Bai yi imani da yin abu don kawai dacewa da zabe na gaba ba. Abin da ya dame shi kawai shi ne yin abu daidai mai kyau saboda al’ummar da ke tafe, imanin da ya ba shi karfin gwiwar cimma wasu kudurori da wasu ke ganin ba su da farin jini, matukar dai ya gamsu cewa yin hakan kare muradun al’umma mafiya rinjaye.

SA HANNU:
Abdu Labaran Malumfashi,
DG Media.
01/01/2021.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here