TAKARDAR MANEMA LABARAI!

MUKABALAR MALAMAI A KANO;BA A YI WA MALAM ABDULJABBAR ADALCI BA!

Daga kungiyar Marubuta ta Wilaya Writers Association of Nigeria(WIWAN).

Da sunan Allah mai Rahama mai Jikai,Tsira da aminci Allah su tabbata ga Annabi Muhammad da iyalan gidansa tsarkaka da nagartattun Sahabbansa wadanda suka talllafi Ahalul Baiti (as) har ya zuwa ranar busa kaho.

Kungiyar “Wilaya Writers association of Nigeria”(WIWAN) sun bibiyi wainar da aka toya a wajen Mukabalar da aka gabatar tsakanin Malamai yau a Kanon-Dabo.A bisa yadda muka bibiyi wannan mukabalar lallai ba a yi wa Shehin Malami Dr.Abduljabbar Nasiru Kabara Kano adalci ba saboda dalilai masu zuwa:-

1.Duk cikin Malaman da ke kalubalantar salon karantawar Dr.Abduljabbar duk sun gudu,sai yaransu suka turo.

2.Ba a haska Mukabalar kai tsaye ba,wanda hakan yake nuna akwai wata kulalliya a ciki.

3.Ba a bayar da lokaci mai tsawo da Malam Abduljabbar zai kare kan shi ba bisa tuhomomin da Malaman ke yi masa ba,a’a a kowacce tambaya minti 10 a ka ba shi wanda bai wadatar ba.

4.Maimakon a aiwatar da Mukabalar a wani muhalli mai yalwa da al’umma za su shaida,sai aka yi a wani kebantaccen muhalli kuntatacce wanda wasu zababbun mutane kawai aka ba ri suka shiga.

5.Dr.Abduljabbar ya je da littafai guda 500 da zai kare kan shi da su,amma an ki ba shi lokaci mai yalwar da zai sami damar budewa ya karanta su.
Bisa wadannan qwararan dalilan guda biyar,kungiyarmu ke neman a sake bai wa Malam Abduljabbar dama da zai kare kan shi,idan ba haka ba kuma lallai a canza wa wannan haduwar suna,maimakon Mukabala a kira ta da wani abun na daban.

Amincin Allah ya tabbata ga wadanda suka bi shiriya.

Sign:Faridat Husain Mshelia(Ummu jiddah)

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here