TAFARU TA KARE; Najeriya ta shiga tsaka mai wuya…

TA FARU TA ƘARE…

Najeriya ta shiga tsaka-mai-wuya saboda arankatakaf din ribar fetur ta tafi wajen biyan tallafin mai, ‘subsidy’

Hukumar Harkokin Man Fetur ta Kasa (NNPC), ta bayyana cewa ba za ta iya tara wa asusun gwamnatin tarayya ko sisi ba cikin watan Mayu, saboda duk wani kudin da aka samu, sun tafi wajen biyan kudaden tallafin mai, wato ‘oil subsidy’.

NNPC ta fitar da wannan sanarwa a cikin wata wasika da ta rubuta wa Akanta Janar na Tarayya, wato Babban Akawun Gwamnatin Tarayya.

Cikin wasikar, NNPC ta bayyana cewa cikin watan Fabrairu, kudaden shigar da hukumar ta tara daga cinikin danyen mai cikin watan Fabrairu 2021, sun kasa da naira biliyan 111.

Dalilin hakan kenan NNPC ta ce lamarin zai shafi yawan kudaden da hukumar za ta tara wa gwamnatin tarayya cikin watannin Afrilu da kuma Mayu.

Wannan sanarwa za ta zama wata babbar barazana ga tattalin arzikin Najerya, wanda babu komai a cikin sa sai fal da tulin bashi.

Najeriya dai ta dogara ne kusan kacokan a kan kudin fetur wajen gudanarwa da aiwatatar da ayyuka da kuma biyan albashin ma’aikata.

NNPC ta ce za ta kasa biyan kudin ne domin ita ma za ta cike gibin da ake fuskatata tsakanin farashin dakon man ferur daga waje da kuma farashin saukalen sa a bakin ruwan Najeriya.

Wannan wasika da NNPC ta aika wa Akanta Janar na Tarayya, an rubuta ta ne tun a ranar 26 Ga Afrilu, ranar Litinin da ta wuce kenan.

An kuma aika da kwafe-kwafen wasikar zuwa ga Ministar Harkokin Kudade, Kasafin Kudi da Tsare-tsare, Gwamnonin Najeriya da kuma Shugaban Kungiyar Kwamishinonin Kudade na Jihohin Najeriya.

Dama su wadannan kwamishinoni, da su gwamnatin tarayya ke zaman kasafta kudaden da ta ke raba wa tarayya, jihohi da kananan hukumomi duk karshen kowane wata.

“Mu na sanar da cewa NNPC ta samu gibin kudi har naira biliyan 111,966, 456,903.74 a cikin watan Fabrairu, 2021.

“Saboda haka mu na sanar wa AGF, Babban Akanta Janar na Tarayya cewa NNPC za ta zabtare naira 111,966,456,903.74 daga kudaden da za ta bayar na karshen watan Afrilu, wanda ta ke rabawa cikin watan Mayu.

“Hakan ya na nufin a takaice kenan NNPC ba za ta iya bai wa Gwamnatin Tarayya, Gwamnatocin Jihohi da Kananan Hukumomi ko sisi ba kenan a cikin watan Mayu, 2021.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here