TABBAS ZA AYI ZABEN SHUGABANNIN APC …inji bagudu

@katsina city news
Gwamnan jahar kebbi bagudu ya tabbatar ma da Manema labarai a Abuja cewa tabbas za a yi zaben shugabannin jam iyyar APC daga matakin unguwani zuwa na tarayya.
Yace yanzu haka tsarin yadda zaben da kuma Ranakun zai gudana an rubuta su a tsare suna gaban shugaban kasa domin ya duba ya kuma Sanya albarka.
Gwamnan yace an tsara jadawalin zaben yadda ba zai Saba ma dokar hukumar zabe ta kasa ba.
Da aka tambaye shi ko za ayi ta zarce .sai yace ku jira jadawalin zaben .ya fito da tsarin shi , komai na a cikin kundin sake zaben shugabannin.
Duk majiyoyi a fadar shugaban kasa da kuma hedkwatar jam iyyar APC sun tabbatar cewa kwamitin Riko ya tsara zaben baje ta a fai FAI mai makon ta zarce a tsarin zaben na shugabannin jam iyyar APC daga unguwani zuwa tarayya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here