Tabarbarewar Tsaro: Gwamna Masari Ya Bada Mafita

..sanya dokar ta baci ba za ta magance Matsalolin tsaron ba

Mai girma Gwamna Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari ya bada shawarar cewa matakin sanya dokar ta-baci ba za ta magance matsalolin tsaro da kasar ke fuskanta ba, illa ma kawai ta sake dagula al’amurra.

Masari ya ba da wannan shawarar ne a ranar Alhamis yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai na gidan Gwamnati bayan ganawa da Shugaban Ma’aikata na shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, a Fadar Shugaban Kasa, Abuja.

Idan za a iya tunawa, majalisar wakilai a ranar Talata ta nemi Shugaba Muhammadu Buhari da ya gaggauta sanya dokar ta-baci a bangaren tsaro don magance matsalar rashin tsaro a kasar.

A cewarsa,babu wadatar dakarun soji da za a yi amfani da su wajen ayyana dokar ta-baci a kasar saboda ayyukan da ke gabansu a halin yanzu sun sha musu kai, bisa ga haka a nemi wata hanya ta musamman shine mafita.

Don haka gwamnan ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su daina sanya siyasa a cikin al’amuran tsaro, yana mai cewa samar da tsaro a kasar a wannan mawuyacin hali nauyi ne da rataya a wuyan kowa. Ya ce ba za a bar Najeriya ta wargaje ba domin hakan na nufin babbar matsala ga nahiyar Afirka baki daya.

Dangane da fargabarsa a kan cewa Gwamnatin Tarayya ba za ta iya biyan jihohi kasafin kudinsu na watan Mayu ba, Masari ya nemi masu ruwa da tsaki kan lamarin da su yi duk wata mai yiwuwa wajen ganin hakan ba ta faru ba.

A cewarsa, matukar jihohi da kananan hukumomi za su tsinci kansu cikin rashin samun kasafin kudin wata daga gwamnatin tarayya, hakan na iya kara rura wutar matsalar tsaro da ake fama da ita a kasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here