Wani yanayi ne na ta leƙo ta koma ke faruwa a jam’iyar adawa ta PDP a Jihar Kano, bayan da Adedamola Fanokun, lauyan jam’iyar ya shaida wa wata Babbar Kotun Taraiya a Abuja cewa jam’iyar da ya ke karewa ba ta taɓa maye gurbin shugabannin jam’iyya ƙarƙashin shugabancin Shehu Wada Sagagi ba.

A ranar 29 ga watan Maris ne dai Mai Shari’a Taiwo O. Taiwo ya bada umarni da ta hana jam’iyar rusa shugabancin jam’iyar da kuma kafa shugabannin riƙo har sai ta kammala saurarar shari’ar.

Hakazalika a ranar, sai uwar jam’iyar PDP ta ƙasa ta sa ƙafa ta shure umarnin kotun, inda ta yi gaban kan ta ya rushe shugabancin jam’iyar a matakin jiha, kananan hukumomi da mazaɓu ta kuma kafa kwamiti na mutum 7 a jihar.

Sai dai kuma Hukumar Kula da Zaɓe mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC ta ƙi amince wa da kwamitin riƙon domin biyayya ga umarnin da kotu ta bayar na hana jam’iyar rusa shugabancin Sagagi a Kano.

Sai dai kuma a zaman sauraron ƙarar na yau Alhamis, lauyan jam’iyar, Falokun ya musanta batun cewa jam’iyar ta kafa kwamitin riƙo a jihar.

Da alhakin ya tambayi lauyan jam’iyar a kan rantsar da kwamitin riƙon, sai lauyan ya ce babu wani rantsar da kwamitin riƙo da ya faru a jihar.

Da ga nan se sai alkalin ya tunatar da kayan kan nauyin faɗin gaskiya da ke kansa, inda ya hore shi da ya faɗi gaskiya.

Shi kuwa lauyan ya kafe cewa jam’iyar ba ta rushe shugabancin Sagagi ta kuma kafa kwamitin riƙo ba.

Da ga nan ne sai alkalin ya faɗa wa lauyan da ya gargaɗi jam’iyar a kan ƙin bin umarninsa, inda ya jaddada cewa in dai ya bada umarni a ka ƙi bi, to duk matakin da jam’iyar ta ɗauka sai ta rushe shi da kan ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here