Ta Canja Zane: Kotun Koli Ta Umurci EFCC Ta Gaggauta Mayar Wa Tsohon Daractan First Bank N9bn Din Da Ta Kwace Ma Sa.

Kotun Kolin Nijeriya ta yanke hukuncin cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Nijeriya EFCC ta gaggauta mayar wa tsohon daractan banki First Bank Dauda Lawal makudan kudaden da ta karbe masa ba bisa ka’ida ba.

A shekar 2016 ne hukumar EFCC din ta karbe wa tsohon daractan makudan kudadensa har naira N9,080,000,000.00 da take zargin cewa ya same su hanyar almundaha ne, inda a 2017 babbar kotun Tarayya dake Lagos ta tabbatar da zargin ga wanda ake inda ta umurci, a damka wa wadanda suka shigar da karar wato EFCC kudaden.

Sai shi wanda ake zargin ya daukaka kara a kotun daukaka kara dake shiyar ta Lagos, inda a nan ta wanke shi ta kuma umurci a mayar masa da kudadensa.

Hakan ne ya sa ita ma hukumar ta EFCC ta garzaya zuwa kotun koli domin, ganin ta sami na sarar kwace kudaden, wanda kuma kotun Kolin ta mara wa hukuncin kotun daukaka kara baya, ta tsaya kan cewa hukumar ta EFCC ta gaggauta mayar wa wanda suke zargi makudan kudaden nasa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here