Sunday Igboho: Gobara ta tashi a gidan mutumin da ya umarci Fulani su fice daga Oyo

Ba a san wadanda suka cinna wa gidan wuta ba

Gobara ta tashi a gidan Sunday Igboho, mutumin da ya umarci Fulani makiyaya su fice daga yankin kudu maso yammacin Najeriya.

Rahotanni sun ce da misalin karfe uku na asubahin yau Talata wasu mutane suka cinna wuta a gidan Sunday Igboho.

Sai dai ba ya gidan saboda ya tashi daga can inda ya koma wani gidan, amma dai gidan da aka cinna wa wuta shi ne babban gidansa da ke birnin Ibadan da ke jihar Oyo.

Hotunan da aka wallafa a shafukan intanet da wasu jaridun Najeriya sun nuna yadda wasu bangarori na gidan suka kone.

Ganau sun shaida wa BBC cewa makwabtan Mr Igboho sun kai dauki a yunkurinsu na kashe gobarar.

Kawo yanzu ba a san wadanda suka tashi wuta a gidan dan bangar kabilar Yarbawan ba.

A ranar Juma’a ne babban Sifeton ‘yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu, ya bayar da umarni ga kwamishinar ƴan sandan jihar Oyo, da ta kamo Mr Sunday Igboho Adeyemo wanda aka fi sani da Igboho.

Mai magana da yawun shugaban Najeriya, Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka a shirin BBC na Ra’ayi Riga.

A cewarsa babban sifeton ƴan sandan ya umarci kwamishinar ƴan sandan jihar Oyo Mrs Ngozi Onadeko ta kamo Igboho sanna ta kai masa shi Abuja.

Ana zarginsa da jagorantar wani gungun jama’a wajen korar makiyaya daga jihar Oyo.

Sai dai har yanzu ba a kamo shi ba.

A makon jiya Mr Igboho ya je wani kauye mai suna Igangan da ke Ƙaramar Hukumar Ibarapa ta jihar inda ya jaddada cewa dole duka Fulanin da ke zaune a jihar ta Oyo su tashi bisa zargin da ake yi a yankin cewa su ne suke kitsa garkuwa da mutane da kashe-kashe da kuma wasu laifuka da ke faruwa a can.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here