Advert
Home Tarihin Unguwannin Katsina da Kewaye SULLUBAWA (ZURU'AR GIDAN DIKKO) DA ASALINSU

SULLUBAWA (ZURU’AR GIDAN DIKKO) DA ASALINSU

Gidan Sarkin Sullubawan Katsina Hakimin Gundumar Kaita

Musa Gambo Kofar Soro @Katsina City News

Asalin Sullubawa a Katsina ya faro ne daga Sarkin Tafarki Dahiru. Shi Sarkin Tafarki Dahiru Dane ga Ardon Shuni, watau Mai Garin Shuni Muhammadu Surajo. Sullubawa sunzo Katsina daga Shuni dake Kasar Sokoto a Lokacin Sarakunan Habe.

Muhammadu Gidado shine Mahaifin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko, Kuma shi Muhammadu Gidado shine babban Dan Sarkin Tafarki Dahiru.

Alokacin mulkin Ummarun Dallaje (1807-1835) ne aka nada Malam Dahiru Kakan Sarki Dikko a matsayin Sarkin Tafarkin Katsina. Aikin Sarkin Tafarki shine kula da baki Yan Kasuwa da Kuma karbar Haraji daga wajen su. Wannan Yana daya daga dalilan da yasa Sarkin Tafarki Dahiru ya zauna a Kofar Sauri Katsina.

DURBI Muhammadu Gidado.

Durbi Muhammadu Gidado shine Mahaifin Sarkin Katsina Muhammadu Dikko. Durbi Muhammadu Gidado ya Riki mukamai da dama kamin ya Zama Durbin Katsina, daga cikin Mukaman days rika akwai Sarautar Kankiyan Katsina. Acikin shekarar 1860 ne aka nada Durbi Gidado a matsayin Durbin Katsina. Durbi Muhammadu Gidado ya rasu a shekarar 1882.

SARKI DIKKO

An haifi Sarki Dikko a shekarar 1865, a Unguwar Kofar.sauri Katsina, a lokacin mulkin Sarkin Katsina Muhammadu Bello Dan Ummarun Dallaje. Kamin ya Zama Sarkin Katsina Sarki Dikko ya yayi Sarautu da dama daga cikin su akwai Karshi, Dan Barhim, Durbi da sauransu.

A Lokacin da Turawan Mulkin Mallaka suka zo Katsina a shekarar 1903, Sarki Dikko Yana rike da Sarautar Durbin Katsina, Hakimin Mani. A lokacin ne Sarkin Katsina Abubakar ya hada Turawan mulkin Mallaka da Sarki Dikko, yace masu duk abinda suke nema su Sami Sarki Dikko. Sarki Dikko ya Zama Liasen Officer tsakanin Turawa da Sarkin Katsina Abubakar.

Acikin watan November 1906, Turawan mulkin Mallaka suka umarci Sarki Dikko da ya Zama Acting Emir a Katsina, bayan Turawan mulkin Mallaka sun cire Sarki Yero daga Sarauta. An nada Sarki Dikko Sarautar Katsina a Ranar 25th January, 1907.

Bayan Sarki Dikko ya hau Sarauta, sai ya taso daga gidan Durbi dake Kofar Sauri, ya shiga gidan Korau dake Kofar Soro.

Sarki Dikko ya kawo chanje chanje a Majalissar sa. Mukami na farko daya fara nadawa shine na Wazirin Katsina, ya nada Waziri Haruna a Matsayin Wazirin Katsina na farko. Sannan ya nada dansa watau Muhammadu Sani Gidado a matsayin Durbin Katsina.

Haka Kuma acikin Garin Katsina, bayan an nada Sarki Dikko, an samu wasu mutane, wadanda suka Rika karkace Hula cewa bata zauna ba, maa na basu yarda da nadin da akayima Sarki Dikko ba, sai da Sarki Dikko ya biyo masu ta bayan gida sannan aka samu saukun su.

Sarki Dikko ya samu nasarori da dama a Katsina a lokacin mulkin shi. Daga cikin Ci gaban daya kawo ma Katsina sune. 1. Alokacin mulkin Sarki Dikko ne aka bude Katsina College a shekarar 1923, a Katsina College ne manyan shuwagabannin Arewa na farko sukayi Karatu, daga cikin su akwai Sarsauna Sokoto Sir Ahmadu Bello, akwai Tafawa Balewa, Sir Usman Nagogo da sauran su.

Haka Kuma alokacin Sarki Dikko ne aka bude Medical School ta farko a Arewa wadda ake Kira Medical Class a Katsina.

Sarki Dikko shine Sarki na farko daya fara zuwa Makka a Kasar Hausa Kuma shine Sarki na farko daya fara zuwa England. Da sauransu.

Reference.

1. Luggard S. Dikko Dynasty, Lugga press Katsina 2006.

2. Kagara W. Sarki Dikko, Gaskiya Corporations Ltd Zaria 1951.

3. Munur M. Tarihin Unguwannin Birnin Katsina, Ahmadu Bello University Press Zaria 2015.

Musa Gambo.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

ADMISSION FORM IS AVAILABLE @ SILICON HEIGHT INTERNATIONAL COLLEGE KATSINA.

SILICON HEIGHT INTERNATIONAL, SCHOOL WISHES TO INFORM THE GENERAL PUBLIC THAT,THE SALE OF FORMS INTO NURSERY, PRIMARY AND SECONDARY IS STILL ONGOING. THE SCHOOL...

Gwamna Aminu Bello Masari ya buɗe taron shuwagabannin Majalisun jihohin Najeriya a Katsina…

Mai girma Gwamnan Jihar Katsina ya bude taron shugabannin majalisun Dokokin Jihohin Najeriya (36) a kwata na uku, da Jihar ta dauki bakunci. Taron da...

Jihar Katsina ta amshi bakuncin Kakakin majalisun Dokokin Jihohin kasar (36).

A cikin shirye, shiryen gudanar da Babban taron Kungiyar wanda ta sabayi lokaci bayan lokaci, domin tattauna al'amurran da suka shafi kasa. Taken taron na...
%d bloggers like this: