SU WA YA KAMATA SU TAIMAKAWA ASHIRU NAGOMA?

Tunda na shigo yanar Gizo yau na ga hotunan Ashiru Nagoma suna yawo na ji babu dadi, don haka na fara neman Wanda na sani a Kannywood domin tattaunawa akan lamarin.
Abu na farko da aka fara sanar da ni daga abokan sana’arsa shine, tun lokacin da ya fara shiga wannan matsalar suka yi yunkurin kai shi asibiti, sai dai a wancan lokacin yan’uwansa suka buga tsalle su ka ce ba su amince ba, har suka yi yunkurin kai wadanda suka yi maganar kara, saboda sun ce an yiwa dan’uwansu kagen hauka, Wanda da kyar aka samu aka kashe maganar.
Tun daga wancan lokacin kowa ke tsoron kara tunkararsa da maganar kai shi asibiti, don haka sai dai idan sun hadu da shi su Dan bashi wani abu, da yawansu sunce har gida su ke zuwa su yi hira da shi su ba shi wani abu, amma suna tsoron kara maganar kaishi asibitin har yanzu da jikin ya yi haka.
Sada Bin Suleiman Usman ya kirani akan yaya za mu taimakawa wannan bawan Allah yanzu, sai na sanar da shi yadda muka yi da wasu abokan sana’arsa, yanzu dai abun da muka yanke shawara da su abokan sana’ar tasa shine; za mu nemi yardar yan’uwansa a rubuce sannan a kaishi asibitin, kamar yadda da yawa daga yan Kannywood din su ka yi alkawarin indai yan’uwansa sun yadda, to za su dauki nauyin yi kaishi asibiti.
Ala bashi duk yadda ake ciki, zan sanar da al’umma Insha Allah. Idan ma abun ya gagaremu ne wanda ba ma fata.
Allah ya sakawa wadanda suka yi yunkurin taimakawa tun farko da Wanda suka yi alwashin yi a yanzu da alkairi Amin.

Copied From
Fauziyya D Sulaiman

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here