Somalia: Ƴan sandan Najeriya 144 sun isa kasar domin wanzar da zaman lafiya

'Yan sandan da Najeriya ta aika Somaila

Wata tawagar ƴan sandan Najeriya mai ƙunshe da ‘yan sanda 144 ta isa ƙasar Somalia domin aikin wanzar da zaman lafiya.

Tawagar, wadda ke karkashin shirin Tarayyar Afirka na samar da zaman lafiya a Somalia da a takaice ake kira (AMISOM), ta isa kasar ne tun ranar Asabar.

Sanarwar da Tarayyar Afirka ta wallafa a shafinta na intanet ta ce ƴan sandan za su kwashe shekara guda suna aiki a Somalia, wadda ke fama da hare-haren mayakan ƙungiyar Al-Shabaab.

“A shekara ɗayan da za su yi za su bayar da shawarwari da kuma dabaru na aiki ga rundunar ƴan sandan Somaila,” in ji sanarwar.

Babban jami’in ƴan sandan da ke kula da tsare-tsare na AMISOM, Daniel Ali Gwambal ya ce za a tura ‘yan sanda 30 zuwa birnin Beletweyne da ke jihar HirShabelle State, yayin da sauran za su gudanar da aiki a matakai daban-daban a birnin Mogadishu.

Ayyukan da ƴan sandan za su yi sun hada da tsaron manyan mutane, atisaye da kuma taimaka wa rundunar ƴan sandan Somalia wajen aikin wayar da kan jama’a, da aikin sintiri tare da ‘yan sandan ƙasar da kuma tabbatar da tsaro a wurare na musamman.

Tawagar ‘yan sandan na isa Somalia ne a yayin da Najeriya ke ci gaba da fuskantar kalubale na tsaro a sassa daban-daban na kasar lamarin da wasu ke ganin raguwar dabara ce.

A baya bayan nan mutanen da ake zargi masu fafutukar ballewa daga Najeriya ne na kungiyar IPOB sun matsa wajen kai hare-hare kn ofisoshin ‘yan sanda a kudu maso gabas da kudu maso kudancin kasar.

Kazalika ‘yan sandan na ci gaba da fafatawa da masu garkuwa da mutane da ‘yan fashin daji da suka addabi arewa maso yammacin kasar, baya ga wadanda suke taimaka wa sojoji wajen yaki da mayakan Boko Haram a arewa maso gabashin kasar.

Wata 'yar sandan Najeriya

'Yan sandan Najeriya da aka aika Somalia

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here