Home Sashen Hausa Sojojin saman Najeriya sun yi luguden wuta a kan yan bindiga a...

Sojojin saman Najeriya sun yi luguden wuta a kan yan bindiga a dajin Kaduna

Sojojin saman Najeriya sun yi luguden wuta a kan yan bindiga a dajin Kaduna

An kashe ‘yan bindiga da dama yayin da jiragen sama ke gudanar da aikin leken asiri a wurare a jihar Kaduna.

Jiragen saman rundunar sun ragargaji ‘yan fashi a garuruwan Rahama, Tami, Sabon Birni, Galadimawa, Ungwan Farinbatu, Sabuwa, Kutemeshi, Gajere, Sabon Kuyello, Dogon Dawa, Ngade Allah, Kidandan, da kuma yankunan da ke kusa da karamar hukumar Birnin Gwari da Giwa.

Samuel Aruwan, Kwamishinan ma’aikatar tsaron cikin gida na jihar Kaduna, ya bayyana a ranar Laraba, cewa bayanan aikin da aka gabatarwa Gwamnatin Jihar ya nuna cewa duk da cewar an gudanar da cikakken bincike a kan yankin baki daya, ba a ga wani abu ba.

Tawagar sun ci gaba da gudanar da aiyuka a Sabon Madada, Babban Doka, Gwaska, Gajere, da kuma garuruwan da ke kusa da su. A Sabon Madada, an ga ‘yan fashi tare da shanu da yawa suna gudu daga garin a hanyar zuwa gabashin wurin. Nan take aka fafata da su sannan aka kashe su.

Sauran wuraren sun bayyana cikin kwanciyar hankali ba tare da fuskantar wata barazanar ba Vanguard ta ruwaito. Gwamna Nasir El-Rufai ya godewa matukan jirgin saboda aikin da suka yi ya kuma ya yaba da kokarinsu a yankunan.

Za a ci gaba da aikin sintiri ta sama a yankin gaba ɗaya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

An yanke wa ‘yan Najeriya biyu hukuncin kisa a Ghana

An yanke wa 'yan Najeriya biyu hukuncin kisa a Ghana ‘Yan Najeriya biyu za su fuskanci da hukuncin kisa ta hanyar rataya a ƙasar Ghana...

Darakta Ashiru na goma ya warke daga ciwon da ke damun sa bayan likitoci sun tabbatar da hakan

Fitaccen darakta a masana'antar shirya fina finan Hausa ta KANNYWOOD Ashiru Na goma ya fito daga Abisiti, bayan Likitoci sun tabbatar da cewa yasamu...

Gwamnatin Kano ta Dakatar da muƙaba da Sheikh Abduljabbar

Yanzu-Yanzu: Wata kotun majistari da ke Gidan Murtala a Kano ta dakatar da gudanar da muqabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Kabara da sauran malamai, kuma...

Restoring Sanity at Nigerian Ports with Electronic Call-up System

Restoring Sanity at Nigerian Ports with Electronic Call-up System By Danjuma katsina Since July 2016, the Nigerian Ports Authority (NPA) under the leadership of Hadiza Bala...

Ma’aikatan tarayya za su ci gaba da aiki daga gida a Najeriya

Ma'aikatan tarayya za su ci gaba da aiki daga gida a Najeriya Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta umarci ma'aikata a mataki na 12 zuwa ƙasa da...
%d bloggers like this: