Dakarun Nijeriya sun daƙile wani hari da ƴan Boko Haram da ISWAP su ka shirya kaiwa a kan Buni-Yadi da ke Ƙaramar Hukumar Gujba a Jihar Yobe a yau Lahadi da rana.

Hakan ne ya sanya murna ta ɓarke a garin, inda mazauna su ka riƙa jinjinawa sojojin a bisa daƙile harin da su ka yi.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa sojojin ƙasa ne su ka fafata da ƴan ta’addan, yayin da jirgin sojin sama kuma ya na yo luguden wuta ta sama a kan ƴan ta’addan da su ka tunkari Buni-Yadi ɗin a kan motoci masu ɗauke da bindiga.

Wani manomi, wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce ya hangi ƴan Boko Haram ɗin suna tsallaka wata ƙorama da ababan hawan su.

“Mun gan su suna ƙoƙarin haure koramar nan da ga yankin Arewa, amma mota ɗaya ce ta iya haurewa.

“Nan su ka bar sauran motocin su ka wuce zuwa Buni-Yadi a ƙafa. Amma daga cikin su da dama da suka haure ruwan, uku ne kawai su ka dawo a raye,” in ji manomin.

Haka-zalika wata majiya da ga ɓangaren tsaro ta tabbatar da cewa an ƙwace motar su mai ɗauke da bindiga, sannan an kashe ƴan Boko Haram ɗin da dama.

Majiyar ta ƙara da cewa an lallata da yawa da ga cikin motocin na su masu ɗauke da bindiga.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here