Advert
Home Sashen Hausa Sojojin Najeriya sunce sun kashe Boko haram da dama-BBC

Sojojin Najeriya sunce sun kashe Boko haram da dama-BBC

Sojojin Najeriya sun ce sun kashe ‘yan Boko Haram da dama

Sansanin 'yan Boko Haram

Hedikwatar tsaron Najeriya ta ce dakarun rundunarta ta Operation Fire Ball sun yi nasarar kashe ‘yan ƙungiyar Boko Haram da dama.

Wani saƙo da rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter a yau Talata ya ce an ƙona motoci masu ɗauke manyan bindigogi da yawa da kuma ƙwato harsasai.

Sai dai ba ta yi wani ƙarin bayani ba game da lokaci da kuma inda aka kai harin, haka nan adireshin da ta maƙala na shafinta na intanet a jikin saƙon mai ɗauke da hotuna ba ya aiki.

Har wa yau, rundunar ta ce wasu dakarun sun yi kama wasu da ake zargin ‘yan bidniga ne a garin Gohono da ke Ƙaramar Hukumar Tangaza ta Jihar Sokoto.

Sanarwar da Manjo Janar John Enenche ya fitar ta ce an ƙwace bindigogi daga hannun Abubakar Mohammed da kuma Ansi Usman Janare bayan kama su ranar Lahadi.

Social embed from twitter

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

WHAT SECTORS OF THE GLOBAL ECONOMY DID NIGERIA ENGAGE MORE IN LAST YEAR?

WHAT SECTORS OF THE GLOBAL ECONOMY DID NIGERIA ENGAGE MORE IN LAST YEAR? #PositiveFactsNG This infograph below shows us what sectors of the global economy Nigerian...

NEW INFRASTRUCTURE FOR THE NIGERIAN NAVAL BASE IN AKWA IBOM STATE!

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/257872623095929/