Sojojin Najeriya ‘sun kashe ‘yan fashi 48, sun ƙwato mutum 18’

Dakarun sojan Najeriya sun kashe ‘yan fashin daji aƙalla 48 a Jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, a cewar kakakin rundunar.

Cikin wata sanarwa a yau Litinin, Janar Mohammed Yerima ya ce dakarun na Runduna ta 8 sun kashe ‘yan bindigar ne a yankunan Bayan Ruwa da Jaya da Kadaya na jihar.

Kazalika sojojin sun raunata wani jagoran ‘yan fashin mai suna Jummo a ƙafa. Sai dai sanarwar ba ta bayyana lokacin da suka kai hare-haren ba.

Haka nan, sun yi nasarar ceto mutum 18 daga hannun ‘yan fashin tare da ƙwace makamai da suka haɗa da bindigar AK-47 guda takwas da G3 ɗaya da kuma mashinga guda ɗaya.

A watan Maris ne rundunar ta ƙaddamar da wani shiri mai suna Operation Tsare Mutane domin ci gaba da zaƙulo ‘yan bindigar da ke addabar yankin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here