Sojoji sun daƙile harin Boko Haram na son sace fasinjoji a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri

sojin Najeriya

Duk da cewa an daƙile harin ƴan ta’addar, wani jami’in leƙen asirin soji ya ce sai da aka ceto waɗansu fasinjojin bayan afka musun da suka yi.

Kafar yaɗa labaran PR Nigeria ta ruwaito cewa nan da nan aka tattaro dakarun runduna ta 212 Battalion Garrison daga Jakana da Goni Masari don raka wasu daga cikin fasinjojin da suka taso daga Damaturu zuwa Maiduguri.

Majiyar leƙen asirin ta ce: “Ƴan ta’addan, waɗanda suka zo gwammansu dukkansu sun je ne cikin baƙaƙen kaya da kuma manyan motoci.

“Suna kuma ɗauke da makamai, sannan wasunsu sun shafa gawayi a fuskokinsu.

“Sun tare hanyar ne da niyyar sace fasinoji da kuma kai wa sojoji hari.”

Sai dai PRNigeria ta ce ba za ta iya tabbatar da ko maharan sun yi nasarar sace mutane ba ko a’a kafin zuwan dakarun tsaron.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here