SOCIAL MEDIA BATADA WATA MATSALA, MASU AMFANI DA ITA NE KEDA MATSALA- Farfesa Mainasara Yaqubu Kurfi

Me bawa Gwamna Masari Shawara akan Harkokin Siyasa Hon. Kabir Sha’aibu

Zaharaddeen Mziag @Katsina City News

Shehin Malami kuma shugaban Sashen koyadda Aikin Jarida na Jami’ar Bayero dake Kano, Farfesa Mainasara Yaqubu Kurfi yayi wannan Kalaman a wajen Taron kammala Horas da ma’abota kafafen sada zumunta na Zamani (Social Media)

Farfesa yayi kira ga Ɗaliban da suka samu Horon, da makarantar Kimiyya da Fasaha ta Hassan Usaman Katsina Polytechnic tayi masu na tsawon wata uku, da su yi aiki da abinda aka koya masu domin tsaftace kafar ta sadarwa, yace;

“Social Media ba kamar sauran kafafen sadarwa namu na gargajiya take ba, Irin Rediyo, Talabijin da Jarida domin su waɗannan sunada wani tsari (Book Keeping) da ake tantance Labari kafin a yaɗashi ga al’uma shiyasa bazaka taɓa samun labarun kanzon kurega a cikinsa ba”. Yace

“Akwai ƙa’idoji da Dokoki wanda kuma nasan duk an karantar daku su, don haka abinda ya rage maku’ aiki da su. Farfesa yace kofa a buɗe take ga duk me buƙatar ƙara faɗaɗa karatunsa tun daga matakin Digiri na ɗaya da na biyu zuwa Ph.D kofa a buɗe take zasu bashi Addmission a Bayero University domin wasala karatunsa.

Da yake maida jawabi a wajen taron, tsohon Ɗan majalisar Tarayya me wakiltar Rimi Charanchi da Ɓatagarawa kuma me bawa Gwamnan Katsina shawara akan Siyasa Hon. Kabir Shi’aibu, yasha Al’washin dorewar karatun, inda yace “zai bawa Gwamna Aminu Masari shawara cewa kamar yanda aka ɗauki nauyin mutum ɗari suka samu wan’nan Ilimin yakamata duk shekara, ayi irin haka ta yanda za’a samu masu mu’amula da kafafen sada zumunta ɗari-ɗari a kowane yanki (Zone) na jihar katsina idan akai haka ana saran za’ai maganin shirme da shiriritar da ke faruwa a kafar ta sada zumunta.

Daya yake faɗin amfani da tasirin Social Media Hon. Sha’aibu yace “Alokacin da yake Ɗan majalisar Tarayya’yan Social Media sun fara yimasa surutu cewa baya aikin komi, sun yi zaɓen Tumun Dare. Ko da yagani sai ya tsaya yayi nazari akan maganganun nasu, hakan yasa bai sauka daga kujerarsa ta Majalisa ba saida ya samar wa sama da Mutum ɗari huɗu aiki, musamman ɓangaren koyarwa, saida takai a yankunan da yake wakilta babu me Masters ko ɗaya duk ya samar masu da aiki a jami’o,i. Yace; wannan tasiri ne na Social Media.

Taron wanda ya gudana a Sashen koyar da aikin Jarida na Hassan Usman Katsina Polytechnic a Ranar Lahadi 27/06/2021 ya samu halartar manyan baki Daktoci malaman jami’a da ‘yan Siyasa.

Dr. Sama’ila Balarabe

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here