DA DUMI-DUMI | Siyasar ma zan shige ta insha Allahu Ta’ala. – Dr. Isa Ali Pantami.

Ministan sadarwa da bunkasa tattalin arziki ta hanyar zamani na kasar Najeriya, Dr. Isa Ali Pantami, ya maida martani akan masu sukar sa game da shiga harkokin siyasa.

Pantami ya maida martani ne a cikin wani faifan Bidiyo da ya yadu a kafar sada zumuntar zamani a wajen karatun sa da yake gabatarwa a masallacin Annur dake garin Abuja., inda yace “Siyasar ma insha Allahu Ta’ala a ba shi lokaci zai shige ta, tunda dokar kasa bata haramta masa shiga siyasar ba”

“Tunda babu Ayar Al-qur’ani da ta hana ni kuma ni dan Najeriya ne ina da ‘yancin shiga siyasa” Inji Dr. Isa Ali Pantami.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here